Rundunar 'Yan Sanda Ta Cafke Jami'anta Da Ke Gadin Tsohon Gwamna, An Bayyana Dalili

Rundunar 'Yan Sanda Ta Cafke Jami'anta Da Ke Gadin Tsohon Gwamna, An Bayyana Dalili

  • Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ɗauki mataki kan jami'anta da ke aikin kare lafiyar tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello
  • Rundunar ta cafke tare da tsare jami'an ƴan sandan bisa zargin cewa sun taimaki tsohon gwamnan ya tsere lokacin da jami'an EFCC suka yi ƙoƙatin cafke shi
  • Jami'an hukumar EFCC dai sun je har gidan Yahaya Bello da ke Abuja domin cafke shi amma ba su yi nasara ba bayan ya samu ya sulale

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Rundunar ƴan sandan Najeriya ta tsare wata jami'ar ƴan sanda wacce ta kasance dogarin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Jaridar The Punch ta ce an cafke ƴar sandan ne tare da sauran ƴan sandan da ke tare da tsohon gwamnan, inda ake tsare da su a sashen binciken manyan laifuka da ke Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Kusan Mutum 50 a Garuruwa 3 a Jihar Katsina

An cafke 'yan sandan da ke tare da Yahaya Bello
Rundunar 'yan sanda ta tsare jami'anta da ke tare da Yahaya Bello Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Kama su tare da tsare su ya biyo bayan umurnin da sufeto janar na ƴan sanda Kayode Egbetokun ya bada na janye su daga wajen tsohon gwamnan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka tsare ƴan sandan?

Jaridar Daily Post ta ce manyan jami'an ƴan sanda da suka nemi a sakaya sunan su, sun bayyana cewa an cafke ƴan sandan ne bisa zargin sun taimaki Yahaya Bello ya tserewa kamu daga hannun jami'an hukumar EFCC.

Wani majiya ya bayyana cewa:

"ADC da sauran ƴan sandan da ke tare da Yahaya Bello an cafke su tare da tsare su."
"An cafke su bisa umurnin sufeto janar na ƴan sanda kan zargin cewa sun taimaka wajen tserewar da tsohon gwamnan ya yi daga kamun jami'an EFCC a ranar Laraba.

Wani majiyar ya sake bayyana cewa:

"ADC ɗin Yahaya Bello da sauran ƴan sandan da ke tare da shi an kawo su ofishin ƴan sanda da safe inda aka tsare su bisa taimakawa tsohon gwamnan ya tsere."

Kara karanta wannan

Gwamna Ododo ya hana a cafke Yahaya Bello? Gaskiya ta bayyana

Ododo bai taimaki Yahaya Bello ba

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamisɓinan ƴada labarai na jihar Kogi ya musanta cewa Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar ya taimakawa Yahaya Bello ya tsare daga kamun hukumar EFCC.

Kingsley Fanwo ya bayyana cewa iƙirarin da hukumar EFCC ta yi na gwamnan ya taimaka Yahaya Bello ya sulale babu ƙamshin gaskiya a cikinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel