Jam'iyyar APC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin Gwamna a Jihar Ondo

Jam'iyyar APC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Fidda Gwanin Gwamna a Jihar Ondo

  • Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya zama ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamna da za a gudanar a watan Nuwamban 2024
  • Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaɓen fidda gwani na APC bayan ya samu ƙuri'u 48,569 inda ya doke sauran abokan takararsa har mutum 15
  • Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo wanda ya jagoranci kwamitin shirya zaɓen, shi ne ya sanar da sakamakon zaɓen fidda gwanin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya lashe zaɓen fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC da aka gudanar a jihar.

Aiyedatiwa, wanda ya gaji marigayi Rotimi Akeredolu a watan Disamba, ya yi nasara kan ƴan takara 15 a zaɓen fidda gwanin da aka gudanar.

Kara karanta wannan

Murna yayin da malamin addinin da 'yan bindiga suka sace ya shaki iskar 'yanci

Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaben fidda gwani
Lucky Aiyedatiwa ya zama dan takarar APC a zaben gwamnan Ondo na watan Nuwamban 2024 Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Masu son takarar gwamnan Ondo a APC

Bayan Aiyedatiwa, waɗanda suka fafata a zaɓen sun haɗa da Jimoh Ibrahim, Olusola Oke, Wale Akinterinwa, Diran Iyantan, Dayo Faduyile, Gbenga Edema, Jimi Odimayo da Isaac Kekemeke.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun haɗa da Olusoji Ehinlanwo, Olugbenga Edema, Funmilayo Waheed-Adekojo, Akinfolarin Samuel, Ohunyeye Felix da Morayo Lebi, Garvey Iyanjan da Judith Omogoroye, Ifeoluwa Oyedele.

APC: Ƙuri'u nawa Gwamna Aiyedatiwa ya samu?

A cewar Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi, shugaban kwamitin shirya zaɓen mai mutum bakwai, Aiyedatiwa ya samu ƙuri’u 48,569, yayin da abokin hamayyarsa Akinfolarin ya samu ƙuri’u 15,343, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Olusola Oke, ya zo na uku da ƙuri’u 14,915, Jimoh Ibrahim ya samu ƙuri’u 9,456 inda ya zo na huɗu, yayin da Akinterinwa wanda ya zo na biyar ya samu ƙuri’u 1,952.

Gwamna Aiyedatiwa ya yi nasara a ƙananan hukumomi 16 cikin 18 da ake da su a jihar Ondo, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Ana cikin takaddamar Ganduje, 'yan APC 1000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP a Kano

A halin da ake ciki dai wasu daga cikin ƴan takarar sun ƙi amincewa da sakamakon zaɓen wanda wasu fusatattun ƴan jam’iyyar APC suka bayyana a matsayin shirme.

Kwamishina ya sha duka wajen zaɓe

A wani labarin kuma, kun ji cewa kwamishinan lafiya na jihar Ondo, Banji Ajaka, ya sha dukan tsiya a wajen zaɓen fidda gwanin gwamnan jihar na jam'iyyar APC.

Wasu fusatattun ƴan APC ne suka yi masa duka bayan sun zarge shi da ɓoye takardar sakamakon zaɓen na mazaɓar Ugbo ta uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel