Majalisa Ta Yi Magana Kan Batun Tsige Gwamna Usman Ododo na Kogi

Majalisa Ta Yi Magana Kan Batun Tsige Gwamna Usman Ododo na Kogi

  • Majalisar dokokin jihar Kogi ta yi magana kan buƙatar da aka yi ɓa ta fara shirin tsige gwamnan jihar, Ahmed Usman Ododo
  • Babban sakataren yaɗa labarai na kakakin majalisar ya ce ba su samu wata wasiƙa wacce ta buƙaci a tsige gwamnan daga muƙaminsa ba
  • Ya yi nuni da cewa babu wani dalilin da zai sanya a tsige gwamnan saboda zargin da ake yi masa ba wanda ya tabbatar da shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Lauyan kare haƙƙin bil’adama, Deji Ajare, ya buƙaci kakakin majalisar dokokin jihar Kogi, Umar Yusuf, ya fara shirin tsige gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo.

Deji Ajare ya buƙaci hakan ne bisa zarge-zargen rashin ɗa’a da kuma yin amfani da muƙaminsa ta hanyar da ba ta dace ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Ododo ya hana a cafke Yahaya Bello? Gaskiya ta bayyana

An bukaci a tsige Ahmed Usman Ododo
Majalisa ta yi magana kan batun tsige Gwamna Usman Ododo Hoto: @OfficialOAU
Asali: Twitter

Ajare ya yi wannan kiran ne a wata wasiƙa da ya aika wa shugaban majalisar, ta hannun magatakardar majalisar a ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar Daily Post.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, yin amfani da ayarin motocin gwamnan wajen ɓoye tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya kai ga ba mai laifi kariya, hana ruwa gudu, da kuma yin amfani da dukiyar jihar ta hanyar da ba ta dace ba.

Me majalisa ta ce kan tsige Ododo?

Jaridar The Punch ta ce babban sakataren yaɗa labarai na kakakin majalisar, Mohammed Yabagi, ya ce magatakarda ko shugaban majalisar ba su samu wannan wasiƙar ba.

Ya ƙara da cewa har yanzu majalisar bata ga wasu ƙwararan dalilai da za su sanya a yi yunƙurin tsige gwamnan ba kuma babu wata shaida da ta nuna gwamnan ya hana jami’an tsaro cafke Yahaya Bello.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta yi barazanar hada-kai da sojoji domin kamo tsohon gwamnan APC

"Kowa a cikin jama'a yana da ra'ayinsa game da lamarin. Sai dai majalisar ba ta ga wani dalili ba, babu ɗaya daga cikin ƴan majalisar da ke wurin, kuma babu ɗaya daga cikinsu da ya ga Gwamna yana ƙoƙarin hana jami’an tsaro yin aikinsu."
"Majalisa tana goyon bayan dukkanin hukumomin ami'an tsaro. Ba mu ga wani dalili da zai sanya mu fara yunƙurin tsige gwamna ba."

- Mohammed Yabagi

Batun Gwamna Ododo ya taimaki Yahaya Bello

A wani labarin kuma, kun ji cewa Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya ce Gwamna Usman Ododo bai taimaki magabacinsa, Alhaji Yahaya Bello, wajen tserewa kada jami'an tsaro su cafke shi.

Fanwo ya ce Ododo a tsaye yake wajen kiyaye dokokin ƙasar nan tare da mutunta su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel