Duniya Labari: An Yi Babban Rashi a Katsina, Gwamna Radda Ya Shiga Jimami

Duniya Labari: An Yi Babban Rashi a Katsina, Gwamna Radda Ya Shiga Jimami

  • Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya nuna alhininsa kan rasuwar Hajiya Hauwa (Maijeddah) Abdulkadir Mamman Nasir
  • Marigayiyar ta kasance matar shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Katsina, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir
  • Gwamna Radda ya nuna kaduwarsa kan rasuwar marigayiyar inda ya aika da sakon ta'aziyyarsa tare da bayyana kyawawan halayenta

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Gwamna Dikko Radda ya sanar da rasuwar matar shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Katsina, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir.

Gwamna Radda ya sanar da rasuwar Hajiya Hauwa (Maijeddah) ne a ranar Laraba, 15 ga Afrilun 2026.

Matar shugaban ma'aikatar fadar gwamnatin Katsina ta rasu
Hajiya Hauwa Abdulkadir Mamman Nasir da Gwamna Dikko Umaru Radda na Katsina Hoto: @dikko_radda
Source: Twitter

Gwamna Radda ya sanar da rasuwar marigayiyar ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.

Matar shugaban ma'aikatan fadar gwamnati ta rasu

Dikko Radda ya bayyana rasuwarta a matsayin rashi mai raɗaɗi ga danginta da dukkanin mutanen da mutuwar ta shafa.

Kara karanta wannan

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce rufin asirin jama'a na cikin nasarar APC a 2027

Gwamna Radda ya bayyana marigayiyar a matsayin wadda mutane ke girmamawa saboda kyawawan halayen da take da su.

“Inna lillahi wa inna ilayhi raji’un"
"Cikin tsananin baƙin ciki na samu labarin rasuwar Hajiya Hauwa (Maijeddah) Abdulkadir Mamman Nasir, matar shugaban ma'aikatan fadar gwamnati na, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir."
"Rasuwarta babban rashi ne mai raɗaɗi ba kawai ga danginta ba, har ma ga dukkanmu da muka san ta a matsayin mace mai tawali’u, mutunci, da halaye na gari. Mutane suna girmama ta saboda kyautatawarta, kyakkyawar dabi'a, da kuma yadda take zama da mutane cikin fara’a."

- Gwamna Dikko Umaru Radda

Gwamna Radda ya yi ta'aziyya

Gwamna Radda ya bayyana cewa rasuwarta za ta bar babban gibi wanda za a dauki lokaci ba a cike shi ba.

Hakazalika ya mika sakon ta'aziyyarsa ga Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, danginta da sauran mutanen da rashinta ya shafa.

Ya kuma yi mata addu'ar samun rahamar Allah Madaukakin Sarki da shiga gidan Aljannah. Gwamnan ya kuma yi addu'ar Allah ya ba da hakuri ga dukkanin mutanen da rashinta ya shafa.

Kara karanta wannan

Ana son ba shugaban kasa, gwamnoni damar yin wa'adin shekara 6

Gwamna Dikko Umaru Radda ya yi ta'aziyya
Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina Hoto: Ibrahin Kaulaha Mohammed
Source: Facebook
"Wannan rashi ya bar babban gibi da za a ji shi sosai. A madadin gwamnati da al’ummar jihar Katsina, ina miƙa ta’aziyyata ga Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, daukacin dangi, ’yan uwa, abokai, da sauran mutanen da wannan rashi ya shafa."
"Ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki (SWT) Ya yafe mata kura-kuranta, ya faɗaɗa kabarinta, Ya ba ta hutu na har abada, kuma ya shigar da ita Aljannatul Firdaus. Ina kuma roƙon Allah Ya ba danginta juriya da haƙuri na jure wannan babban rashi.”

- Gwamna Dikko Umaru Radda

Shugaban hukumar KSWB ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban hukumar samar da ruwan sha ta jihar Katsina (KSWB), Injiniya Tukur Tingilin, ya yi bankwana da duniya.

Tukur Tingilin ya rasu ne sakamakon hatsarin mota da ya ritsa da shi a ranar Alhamis, 26 ga watan Fabrairun 2026.

Gwamna Dikko Umaru Radda ya bayyana rasuwar marigayi Injiniya Tukur Tingilin a matsayin babban rashi ga jihar Katsina.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng