Dangote Ya Fadi Dalilin Zaftare Farashin Man Dizal Zuwa N1,000

Dangote Ya Fadi Dalilin Zaftare Farashin Man Dizal Zuwa N1,000

  • Aliko Dangote wanda ya fi kowa arziƙi a nahiyar Afirika ya bayyana dalilin da ya sa matatar man fetur ɗinsa ta zaftare farashin man dizal
  • Dangote ya ce an rage farashin ne domin ya yi sauƙi da taimakawa talakawan ƙasar nan wajen siyan kayyyaki masu arha
  • A cewarsa rage farashin zai sanya aka ƙara samar da ayyukan yi tare da rage tsadar kayayyaki a kasuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Gombe - Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana dalilin da ya sa matatar man Dangote ta karya farashin man dizal zuwa N1,000.

Dangote ya ce an zaftare farashin ne domin ya yi sauƙi da kuma rage tsadar kayayyaki ga talakawan ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya kawo muhimman dalilai 2 da suka haddasa rashin tsaro a Najeriya

Dangote ya rage farashin man dizal
Dangote ya ce rage farashin man dizal zai sanya kayayyaki su yi arha Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

Ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai jiya a Gombe bayan halartar ɗaurin auren ɗiyar abokin kasuwancinsa, Alhaji Umaru Kwairanga, Sarkin Fulanin Gombe, cewar rahoton jaridar Nigerian Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Dangote ya rage farashin dizal?

A cewarsa, arhar farashin dizal zai taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar nan, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Ya bayyana cewa, ta hanyar rage farashin man dizal, ƴan kasuwa za su samu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, wanda a ƙarshe zai haifar da ƙaruwar yawan aiki, samar da ayyukan yi da rage farashin kayayyaki.

A kalamansa:

"Idan ka duba, a zahiri dizal yana shafar rayuwar kowa. Tsadar kayayyaki kamar su tumatur a wajenmu a Legas saboda tsadar jigilarsa ne, sannan ko mu idan za mu samar da wani abu, dizal ne abu mai tsada. Da muka duba hakan, sai mu yanke shawarar yadda za mu rage tsadarsa."

Kara karanta wannan

Taron NEC: Babban jigo ya buƙaci shugaban PDP na ƙasa ya yi murabus nan take

Ya ci gaba da cewa, akwai mutanen da suka daɗe suna yin sana’ar kuma suna cin riba, don haka ya yanke shawarar cewa man dizal bai kamata ya wuce N1,000 ba, wanda hakan kusan ragin kaso 60%.

"A wurare irin su Borno da Bauchi ana siyar da shi tsakanin N1,700 zuwa N1,800, amma ina da tabbacin nan da ƴan kwanaki masu zuwa ba za ku sayi dizal a sama da N1,000 a ko’ina a Najeriya ba."

- Aliko Dangote

Tinubu ya yabawa Dangote

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi martani bayan Aliko Dangote ya rage farashin litar mai.

Tinubu ya yabawa attajirin bayan ya rage farashin litar dizil daga N1,200 zuwa N1,000 i ya ce hakan zai taimaka wurin rage farashin kaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel