Jigon PDP Ya Bayyana Yadda Peter Obi da Buhari Suka Yi Tarayya a Wajen Halayya

Jigon PDP Ya Bayyana Yadda Peter Obi da Buhari Suka Yi Tarayya a Wajen Halayya

  • An kwatanta Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP) tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta fuskar cimma burinsu
  • Wani jigon jam’iyyar PDP, Rilwan Olanrewaju, ya yi kwatancin yayin da ake zantawa da shi kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar LP
  • Olanrewaju ya ce ya hango rikicin da ke faruwa a jam’iyyar LP, inda ya shawarci Peter Obi ya koma jam'iyyar PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

An kwatanta tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, dangane da yadda suke neman cika burinsu.

Jigo a jam’iyyar PDP, Rilwan Olanrewaju, ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng ta yi da shi.

Kara karanta wannan

Ana cikin takaddamar Ganduje, 'yan APC 1000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP a Kano

An kwatanta Peter Obi da Buhari
Jigon PDP ya ce Peter Obi na da hali irin na Buhari Hoto: @Mbuhari, @PeterObi
Asali: Twitter

An tattauna da shi ne dangane da rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar LP da kuma jita-jitar cewa Peter Obi na iya barin jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jigon na PDP ya shawarci tsohon gwamnan na jihar Anambra da ya koma jam'iyyar PDP.

An shawarci Peter Obi ya koma PDP

Sai dai Olanrewaju ya bayyana cewa zaɓin da yafi dacewa shine Peter Obi ya koma jam’iyyar PDP, inda ya ƙara da cewa ƙwadayinsa na zama shugaban Najeriya za a iya kwatanta shi da irin na tsohon shugaban ƙasa Buhari.

Ya kuma ce jam’iyyar LP da jam’iyyar APC suna kamanceceniya da juna wajen aƙida.

"Jam’iyyar LP tana kama da APC, aƙidarsu iri ɗaya ce. Haka kuma Peter Obi yana kama da Buhari, domin yakin neman zaɓensu da ƙosawarsu iri ɗaya ce."

Kara karanta wannan

Kwankwaso da 'yan Kwankwasiyya sun ci amanata, wanda ya kafa NNPP ya fame tsohon 'yambo

"Ya kamata Peter Obi ya dawo jam'iyyar PDP. Na hango rugujewar LP amma ɓan taɓa sanin abin zai zo da sauri kamar haka ba. Yin cikakkiyar adawa ba abu ba ne mai sauƙi, shiyasa na yi dariya lokacin da na ga magoya bayan LP suna yi wa PDP shaguɓe."
"Saboda ba su san yadda ake tafiyar da jam'iyya ba. Peter Obi zai fice daga LP amma abin da zai fiye masa shi ne ya dawo PDP maimakon wata ƙaramar jam'iyya, idan har da gaske yana son zama shugaban ƙasa."

- Rilwan Olanrewaju

LP za ta ba Peter Obi takara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar adawa Labour Party (LP) ta bada shawarar tanadar tikitin takarar shugaban ƙasa na zaɓen 2027 ga tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi.

Jam'iyyar ta fara shawarwarin sake tsayar da Obi takara ne yayin da ta ke shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen 2027 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel