'Yan Bindiga da 'Yan Banga Sun Gwabza Fada a Sokoto, An Hallaka Mutum 6

'Yan Bindiga da 'Yan Banga Sun Gwabza Fada a Sokoto, An Hallaka Mutum 6

  • An yi arangama tsakanin ƴan bindiga da ƴan sakai a ƙaramar hukumar Gada da ke jihar Sokoto inda aka yi asarar rayuka
  • Rahotanni sun ce faɗan ya fara ne bayan wani ɗan bindiga ya hallaka shugaban ƴan bindiga bayan ya yi ƙoƙarin cafke shi a cikin kasuwa
  • Kisan shugaban ƴan bangan ya jawo ɓarkewar rikici inda aka rasa rayukan mutum shida yayin da wasu da dama suka samu raunuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto -Mutum shida sun rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin ƴan bindiga da ƴan banga da aka fi sani da ƴan sa-kai a ƙaramar hukumar Gada a jihar Sokoto.

Ƴan bangan, a cewar wata majiya a yankin da ta nemi a sakaya sunansa, sun ɗauki fansa ne kan kisan da wasu ƴan bindiga suka yi wa shugabansu, Alhaji Dahiru.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Kusan Mutum 50 a Garuruwa 3 a Jihar Katsina

'Yan bindiga da 'yan banga sun yi fada a Sokoto
Mutum 6 sun rasu a fadan 'yan bindiga da 'yan banga a Sokoto Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Shaidun gani da ido sun ce rikicin ya fara ne a lokacin da wani jagoran ƴan banga a ƙauyen Gidan Hashimu ya yi yunƙurin kama wani barayin shanu da aka gani yawo a kasuwa domin yi yi masa tambayoyi, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindigan ana cikin rikicin sun hallaka shugaban ƴan bangan, wanda hakan ya jawo sauran ƴan bangan ɗaukar fansa.

Ɗaya daga cikin shaidun ya bayyana cewa kafin zuwan ƴan sanda a kasuwar, an hallaka sama da mutum shida.

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Gada, Kabiru Gada, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

"Lamarin ya auku ne lokacin da aka ga wani shugaban ƴan bindiga yana siyayya a kasuwar Gada, inda wasu shugabannin ƴan banga suka gane shi tare da buƙatar a cafke shi domin yi masa tambayoyi.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindinga sun kashe 'yan banga 3 tare da sace mutane masu yawa a wani sabon hari

"Daga nan sai ya yi gardama inda nan take ya harbi shugaban ƴan banga na ƙauyen Gidan Hashimu wanda hakan ya sanya ƴan banga suka kai harin ramuwar gayya kan Fulani."

- Kabiru Gada

Legit Hausa ta samu jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmed Rufai, wanda ya tabbatar da cewa an hallaka mutum shida a yayin rikicin.

A kalamansa:

"Muna ci gaba da gudanar da bincike domin gano masu hannu a lamarin domin su fuskanci hukunci."

Faɗan Hausawa da Fulani

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin hankali a garin Gwadabawa da ke jihar Sokoto, bayan wani rikici ya kaure tsakanin Fulani da Hausawa a yankin.

Mummunan karon ya yi sanadiyar mutuwar mazauna yankin da dama daga bangarorin biyu, ciki harda jami'an tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel