Gwamna Ododo Ya Hana a Cafke Yahaya Bello? Gaskiya Ta Bayyana

Gwamna Ododo Ya Hana a Cafke Yahaya Bello? Gaskiya Ta Bayyana

  • Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kogi ya yi magana kan dambarwar da ake yi kan batun cafke tsohon gwamnan jihar
  • Kingsley Fanwo ya bayyana cewa Gwamna Usman Ododo bai hana a cafke magabacinsa Alhaji Yahaya Bello ba
  • Kwamishinan ya kuma yi nuni da cewa gwamnan Kogi mai bin doka da oda ne tare da mutunta dokokin ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya ce Gwamna Usman Ododo bai taimaki magabacinsa, Alhaji Yahaya Bello, wajen tserewa ka da jami'an tsaro su cafke shi.

Jami’an hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC) sun zagaye gidan Bello da ke Abuja, inda suka so kama shi.

Kara karanta wannan

Majalisa ta yi magana kan batun tsige Gwamna Usman Ododo na Kogi

Usman Ododo ya je gidan Yahaya Bello
Kwamishinan Kogi ya ce Gwamna Usman Ododo bai hana a cafke Yahaya Bello ba Hoto: @OfficialOAU, @OfficialGYBKogi
Asali: Twitter

Amma Gwamna Ododo ya isa wurin, inda bayan sa’o’i da barinsa gidan, an samu labarin cewa Yahaya Bello ya gudu tare da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me kwamishinan ya ce kan cafke Yahaya Bello?

Jaridar Vanguard ta ce da yake magana a wata hira da gidan talabijin na Channels, Fanwo, wanda shi ma yayi aiki a ƙarƙashin Bello, ya ce Ododo a tsaye yake wajen kiyaye dokokin ƙasar nan tare da mutunta su.

"Gwamna Ododo bai taimaka wajen barin Yahaya Bello daga gidansa ba. Iƙirarin da EFCC ta yi ba gaskiya ba ne, ta yi ne kawai domin cimma manufofinta."
"Yahaya Bello ba ya ɓoyewa kowa. Umurnin da kotu ta bada ya kare masa haƙƙinsa."

- Kingsley Fanwo

Fanwo ya yi watsi da iƙirarin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawan, yana mai bayyana su a matsayin marasa tushe domin yaɗa wata manufa, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta ayyana tsohon gwamna a matsayin wanda take nema ruwa a jallo

Ya ƙara da cewa tsohon gwamnan baya ƙoƙarin ɓoyewa kada a kama shi, yana mai nuni da umarnin wata babbar kotun jihar da ta kare Bello daga cin zarafi daga hukumar EFCC.

Umurnin NIS kan Yahaya Bello

A wani labarin kuma, kun ji cewa shige da fice ta Najeriya(NIS) ta sanya tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello cikin wadanda take sanyawa idanu.

Bayar da umurnin na zuwa bayan rundunar ƴan sandan ƙasar nan ta janye jami'anta da ke tsaron tsohon gwamnan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel