Manyan Labarai A Yau
Shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, sun musanta cewa akwai hannunsu a cikin dakatar da Ganduje.
Shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na mazabar Gaduje za su kai ziyara ga shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, a Abuja.
An samu rahoton barkewar wata sabuwar cuta a karamar hukumar Kura ta jihar Kano. Cutar wacce ba a san musababbabinta ba ta salwantar da rayukan mutum 45.
Miyagun 'yan bindiga sun kai sabon harin ta'addanci a wasu kauyukan jihar Kaduna inda suka hallaka mutum uku. Sun kuma yi awon gaba da wasu mutum bakwai.
Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da rage farashin man dizal a kasuwa. A yanzu matatar za ta rika sayar da man dizal a kan farashin N1000 maimakon N1200.
Kakakin majalisar dokokin jihar Kaduna, Yusuf Liman, ya yi magana kan kwamitin da majalisar ta kafa ɗomin bincikar tsohon gwamnan jihar Nasir Ahmaɗ El-Rufai.
Shugaban kamfanin Rainoil, Gabriel Ogbechie, ya yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dawo biyan tallafin man fetur.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmad El-Rufai, ya bayyana cewa gwamnoni na amfani da hukumomin zabe na jihohi domin tafka magudin zabe.
Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta karyata batun dakatar da shugabanta na kasa, Abdullahi Umar Ganduje. Ta dauki mataki kan masu hannu a ciki.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari