Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Banga 3 Tare da Sace Mutane Masu Yawa a Wani Sabon Hari

Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Banga 3 Tare da Sace Mutane Masu Yawa a Wani Sabon Hari

  • Aƙalla ƴan banga uku ne ƴan bindiga suka kashe a ƙauyen Maraban Agyaro da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna
  • Ƴan bindigan sun kuma yi garkuwa da ɗan hakimin ƙauyen a lokacin da ya je ɗibar yashi a ranar Juma’a, 19 ga watan Afirilu
  • An ƙona babura bakwai sannan ƴan bindigan sun gudu da mutum biyar bayan sun farmaki ƙauyen a ranar Alhamis, 18 ga watan Afirilu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun kashe ƴan banga uku, sun ƙona babura bakwai tare da sace mutum biyar bayan sun kai hari ƙauyen Maraban Agyaro da ke jihar Kaduna.

An tattaro cewa harin ya faru ne a mazaɓar Kakangi kan titin Birnin Gwari zuwa Kakangi a yammacin ranar Alhamis, 18 ga watan Afrilun 2024.

Kara karanta wannan

An sheke shugabannin 'yan bindiga 2 a wani kazamar fada a jihar Zamfara

'Yan bindiga sun kai hari a Kaduna
'Yan bindiga sun hallaka 'yan banga a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kakangi a majalisar dokokin jihar Kaduna, Yahaya Musa DanSalio ya tabbatar da faruwar harin kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"An sanar da ni an kashe ƴan banga uku; mutum ɗaya ya ɓata, amma har yanzu muna samun cikakken bayani kan lamarin. Na sanar da gidan gwamnati halin da ake ciki.”

Ƴan bindiga sun sace ɗan hakimin ƙauye

DanSalio ya ƙara da cewa ƴan bindigan sun kuma yi garkuwa da ɗan hakimin ƙauyen Rafin Gora da ke ƙarƙashin wannan mazaɓar da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar ranar Juma’a.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa ɗan hakimin ƙauyen ya je ɗauko yashi ne a kusa da garin lokacin da aka sace shi.

Ya bayyana cewa an sanya jami’an tsaro a Dogon Dawa cikin shiri tun bayan faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wuta, sun kashe ɗalibin jami'a da wasu bayin Allah a Filato

Ƴan bindigan sun kai harin ne a lokacin da mutanen ƙauyen ke hanyar komawa gida bayan sun je kasuwar mako-mako a garin Birnin Gwari.

An bar motar da ke ɗauke da ƴan kasuwar yayin da aka yi awon gaba da mutanen da ke cikinta tare da direban.

Mutum nawa aka sace?

Tsohon shugaban ƙungiyar Cigaban Masarautar Birnin Gwari, Ishaq Usman Kasai, ya bayyana cewa:

"Kimanin mutum huɗu aka kashe a Maraban Agyaro dake kan titin Kakangi-Birnin Gwari. Har yanzu ba mu iya tantance adadin mutanen da aka sace ba waɗanda suka haɗa har da direban motar."

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, ya ce an tura jami’an tsaro zuwa yankin.

Ƴan bindiga sun gwabza faɗa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga masu gaba da juna sun yi mumminm artabu a jihar Zamfara.

A yayin artabun an hallaka shugabannin ƴan bindiga mutum biyu tare da mayaƙa 12 yayin da aka raunata wasu da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel