Jihar Legas
Matatar Dangote ta sayi danyen man Ceiba har ganga 950,000 daga kasar Equatorial Guinea, yayin da NNPC ke tattaunawa da matatar kan tsarin sayen danyen mai da Naira.
‘Yan bindiga sun kashe ɗan takarar APC, Oluwatosin Onamade, a Legas. Bayan harsashi ya gagara shigarsa, sun sassare shi da adda a kai da fuska har ya mutu.
Yayin da ake hasashen haɗaka a zaben 2027, tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya kai ziyara ga Rauf Aregbesola da Fasto Tunde Bakare a Lagos.
Iyalan marigayi Janar Sani Abacha sun gargadi tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida da ya daina bata sunan mahaifinsu musamman a littafinsa.
Tashar wutar lantarki ta kasa ta samu matsala, wanda ya haddasa duhu a wasu yankuna. Kamfanonin rarraba wuta na aiki don dawo da wutar cikin gaggawa.
Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Legas sun kama wasu mutane biyu 'yan kasar Pakistan da suka yi amfani da jirgin sama wajen sace wani mutum a Kano.
Wasu dakarun sojin saman Najeriya a jihar Legas sun dura ofishin rarraba wutar lantarki na Ikeja sun lakadawa mutane duka kan yanke musu wuta a kan bashi.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ƴa gayawa duniya cewa a yanzu yana hutawa ne bayan ya samu nasarar kammala aikin matatar mai.
Shahararriyar jarumar fina-finan Nollywood, Mama Ereko, ta bayyana wahalhalun da ta sha a aurenta inda ta ce mijinta na kawo mata gida a gabanta.
Jihar Legas
Samu kari