Iyalan Abacha Sun Yi Martani ga IBB, Sun Fadi Yadda Marigayin Ya Yeci Rayuwarsa

Iyalan Abacha Sun Yi Martani ga IBB, Sun Fadi Yadda Marigayin Ya Yeci Rayuwarsa

  • Dangin marigayi Janar Sani Abacha sun gargadi tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida da ya daina bata sunan mahaifinsu bayan sakin littafinsa
  • A cewar Mohammed Abacha, babu gaskiya a zargin da IBB ya yi a littafinsa cewa Abacha ne ya soke zaben 12 ga Yunin shekarar 1993 da aka gudanar
  • Sun ce Abacha ba shugaban kasa ba ne lokacin da aka soke zaben, don haka babu dalilin da zai sa a ce shi ke da alhakin hakan saboda bai da alaka da shi
  • Iyalan Abacha sun bayyana cewa marigayin ne ya ceci rayuwar IBB lokacin da rayuwarsa ke cikin hadari, amma bai samu yabo ba a littafin da aka kaddamar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Dangin marigayi shugaban kasa, Janar Sani Abacha, sun yi martani ga Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Kara karanta wannan

Zargin lalata: Akpabio ya yi fallasa, ya fadi rawar da marigayi Abba Kyari ya taka

Iyalan marigayin sun gargadi IBB da ya daina bata sunan Abacha a cikin littafin da ya kaddamar a Abuja.

Iyalan Abacha sun yi martani ga Janar Babangida
Iyalan Abacha gargadi Janar Ibrahim Babangida kan kokarin bata suna marigayin. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

'Ya'yan Abacha sun bukaci IBB ya yi gaskiya

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mohammed Abacha ya fitar a ranar Lahadi 9 ga watan Maris, 2025, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin littafinsa “A Journey in Service” IBB ya zargi Abacha da soke zaben 12 ga Yunin shekarar 1993.

Dangin Abacha sun ce wannan zargi ya janyo cece-kuce a cikin kasa, kuma yana bukatar a bayyana gaskiya domin adalci da tabbatar tarihi.

Sanarwar ta bayyana zargin da cewa karya ne, inda tace “kokarin dorawa Abacha laifi ne wanda ba daidai ba ne kuma ba gaskiya ba.

Sanarwar ta ce:

“Abacha ba shugaban kasa ba ne lokacin da aka soke zaben, IBB ne ke da ikon mulki gaba daya kuma shi ne ya dauki matakin.”

Kara karanta wannan

Ajali ya yi kira: Hatsabibin ɗan bindiga, Shekau ya mutu yayin arangama da ƴan ta'adda

"Mu na bukatar ‘yan Najeriya su “yi hattara da masu kokarin canza tarihi domin son zuciya ko dalilan siyasa.”
“Bai kamata a bata Abacha ba da zarge-zargen da babu tushe, domin kare wadanda suka aikata laifin gaske.”
Iyalan Abacha sun kalubalanci IBB kan soke zaben Abiola
Iyalan marigayi Sani Abacha sun caccaki IBB kan yi wa mahaifinsu sharri. Hoto: John Harrington/Issouf Sanogo.
Asali: Getty Images

'Yadda Abacha ya ceci rayuwar IBB' - iyalansa

Game da yadda Abacha ya ceci rayuwar IBB, Vanguard ta ruwaito danginsa na cewa:

“Lokacin da rayuwar IBB ta shiga hadari, Abacha ne ya zo ya ceci shi, muna bakin ciki da yadda littafin bai bayyana tarihi bisa gaskiya da adalci ba."

Tsohon Soja ya fallasa shirin IBB kan Abacha

Kun ji cewa wani tsohon babban soja a mulkin Janar Ibrahim Babangida Babangida ya caccake shi bayan kaddamar da littafinsa a birnin Abuja.

Janar Ishola Williams mai ritaya ya ce IBB ya shirya Abacha don karɓar mulki kafin soke zaɓen 12 ga Yuni 1993, ba tare da izininsa ba.

A cikin littafinsa, IBB ya amince da cewa MKO Abiola ne ya lashe zaɓen, amma ya ce Abacha ne ya soke nasararsa shi ba tare da izininsa ba a wancan lokaci.

Williams ya ce gwamnatin rikon kwarya da Ernest Shonekan ya jagoranta ba gaskiya ba ce, an shirya wa Abacha hanyar karbar ragamar mulkin kasa ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng