A Karshe, Matatar Dangote Ta Dakatar da Siyar da Mai a Naira, Ta Jero Dalilanta

A Karshe, Matatar Dangote Ta Dakatar da Siyar da Mai a Naira, Ta Jero Dalilanta

  • Matatar Aliko Dangote ta dakatar da sayar da man fetur da naira na ɗan lokaci saboda dalilai na musayar kuɗi
  • Dangote ya ce har yanzu bai samu isasshen danyen mai da aka kayyade da naira daga NNPC ba
  • Kamfanin ya musanta jita-jitar da ke yawo cewa dakatarwar ta faru ne saboda zamba da aka yi a tikitin lodin kaya
  • Ya tabbatar da cewa za a ci gaba da sayar da fetur da naira idan aka samu kayan da aka ware da naira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Matatar Aliko Dangote ta sanar da dakatar da sayar da kayayyakin man fetur da naira na ɗan lokaci.

Wannan sanarwar ta fito ne a cikin wata wasiƙa da aka aike wa ‘yan kasuwar mai a ranar Laraba 19 ga watan Maris, 2025.

Kara karanta wannan

Mutane da dama sun mutu da wata tanka ta yi bindiga a tsakiyar jama'a a Abuja

Matakin da Dangote ya dauka kan siyar da mai a Najeriya
Matatar Dangote ta dakatar da siyar da mai a Naira. Hoto: Bloomberg.
Asali: UGC

Musabbabin daukar matakin matatar Dangote

A cikin wasiƙar da Daily Trust ta samu, kamfanin ya bayyana dalilin da ya sa ya dauki wannan matakin na dakatarwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote ya ce wannan shawara ta zama dole saboda bambanci tsakanin kudin shigar da suke samu da kuma kuɗin da suke amfani da shi wajen sayen danyen mai.

Sanarwar ta ce:

“Mun yanke shawarar dakatar da sayar da man fetur da Naira na ɗan lokaci, wannan mataki ne da ya zama dole don guje wa rashin daidaito tsakanin kuɗin shiga da kuɗin sayan danyen mai, wanda yanzu haka ana biya da dalar Amurka.
“Har yanzu, kudaden da muka samu ta hanyar sayar da mai da Naira sun wuce darajar danyen man da muka samu da aka biya da Naira.
"Saboda haka, dole ne mu daidaita kudin da muke amfani da shi wajen siyarwa da kuma saye."
Matatar Dangote da dakatar da siyar da mai a Najeriya
Matatar Dangote ta soke siyar da mai kan Naira ga yan kasuwa. Hoto: Dangote Industries.
Asali: Facebook

Dangote ya ba yan kasuwa tabbaci

Kara karanta wannan

Dangote zai bar saida fetur a Najeriya, NNPCL ya tsaida yarjejeniyar ciniki da Naira

Kamfanin ya kuma mayar da martani kan rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an dakatar da lodin mai ne saboda wata matsala ta damfara da aka samu a tikitin lodin kaya.

Matatar Dangote ta tabbatar wa ‘yan kasuwa da al’umma cewa suna da niyyar ci gaba da bauta wa kasuwar Najeriya yadda ya kamata da kuma nagarta.

Kamfanin ya ce da zaran sun samu danyen mai daga NNPC da aka kayyade da Naira, za su ci gaba da sayar da fetur da Naira, cewar TheCable.

Kamfanin ya ce:

“Muna godiya da fahimta da haɗin kai daga gare ku a wannan lokaci, za mu sanar da sake dawo da sayar da mai da Naira da zaran an warware wannan matsala"

Kamfanin Dangote na ɗaya daga cikin muhimman sassan da ake sa ran zai taimaka wajen rage dogaro da shigo da mai daga kasashen waje.

Kara karanta wannan

'Za a iya samun karamin yaki a Rivers,' 'Yan Neja Delta sun gargadi Tinubu

Kotu ta dakile korafin NNPCL kan Dangote

Kun ji cewa Kotun Tarayya ta kori korafin NNPCL da ke ƙalubalantar cancantar karar da matatar Aliko Dangote ta shigar kan lasisin shigo da kaya.

Alkalin kotun ya ce kamfanin NNPCL ya karya dokokin shari’a, inda ya kasa gabatar da bayanai da kuma shigar da ƙara marar inganci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.