Dangote Ya Fadi Abin da Ya Sa a Gaba bayan Kammala Aikin Matatar $20bn

Dangote Ya Fadi Abin da Ya Sa a Gaba bayan Kammala Aikin Matatar $20bn

  • Hamshaƙin attajiri a Najeriya da Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana inda akalarsa ta karkata a halin yanzu
  • Dangote ya bayyana cewa a yanzu yana hutawa ne bayan ya kammala aikin matatarsa wacce ta laƙume sama da $20bn
  • Shugaban rukunin kamfanonin na Dangote dai ya gina matatar ne wacce tuni ta fara aiki a yankin Lekki da ke jihar Legas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yi maganna kan abin da ya tasa a gaba.

Aliko Dangote ya bayyana cewa yana hutawa a halin yanzu bayan kammala aikin matatar man fetur da ya gina.

Dangote ya fadi abin da ya sa a gaba
Dangote ya ce yanzu hutawa yake yi Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Hamshaƙin attajirin ya bayyana hakan ne yayin bikin aza harsashin sabon ginin hedkwatar bankin First Bank mai hawa 43 a birnin Eko Atlantic City da ke Legas, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Makusancin Kwankwaso, Buba Galadima ya hango illar saukar farashin abinci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote ya kammala aikin matatar mai

Dangote ya bayyana cewa yanzu yana hutawa bayan samun nasarar kammala aikin matatar da ya yi.

Matatar mai ƙarfin sarrafa gangunan mai 650,000 a kowace rana ta ci sama da dala biliyan 20 wajen ginata, ta kawo sauyi a kasuwar mai da iskar gas ta Afirka da ma duniya baki ɗaya.

A halin yanzu, matatar na fitar da kayayyakin da ta tace zuwa wasu ƙasashen Afirka da yankin Gabas ta Tsakiya.

Dangote ya taɓa bayyana irin ƙalubalen da ya fuskanta wajen gina matatar, wanda ya bayyana a matsayin mafi girman kasadar da ya yi a rayuwarsa, inda ya ce lamarin ya sa ya shiga mawuyacin hali.

Me Aliko Dangote ya sa a gaba yanzu?

Ya yabawa abokinsa Mr Femi Otedola, wanda shi ne shugaban kamfanin FirstHoldCo, saboda ƙoƙarinsa na gina katafaren ginin mai hawa 43 a Eko Atlantic domin zama sabuwar hedkwatar bankin First Bank.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya

Dangote ya ce birnin Eko Atlantic ya zama sabon birni a Legas, kuma kasancewar First Bank a wajen, hakan zai jawo hankalin wasu bankuna su zo su kafa ofisoshinsu a wurin.

Sai dai ya bayyana cewa Otedola ya gayyace shi zuwa birnin Eko Atlantic, amma ya nuna masa cewa hutawa yake yi a yanzu.

“Wataƙila nan gaba, amma ba yanzu ba, domin a halin yanzu ina hutawa. Bayan nasarar kammala aikin matatar mai, ina buƙatar hutu amma zan zo, zan kasance a nan ba da daɗewa ba."
"Don haka ina taya ku murna (Otedola) da dukkanin shugabanni da ma’aikatan First Bank saboda wannan gagarumin yunƙuri na gina katafaren gini a sabon birnin Legas."

- Alhaji Aliko Dangote

Manyan mutane sun halarci taron

Taron aza harsashin ginin hedkwatar ya samu halartar mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, gwamnonin Legas, Ogun da Ondo, Babajide Sanwo-Olu, Dapo Abiodun da Lucky Aiyedatiwa.

Sauran manyan baƙi da suka halarta sun haɗa da mataimakin gwamnan jihar Legas, Dr. Femi Hamzat, tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki da tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori.

Kara karanta wannan

Dangote ya fadi wuraren da za a rika samun fetur dinsa a farashi mai rahusa

Haka kuma wasu attajirai da shugabannin kamfanoni da suka halarta sun haɗa da shugaban kamfanin Pacific Holdings, Dr. Deji Adeleke, shugaban kamfanin Sapetro, Sanata Daisy Danjuma, Gilbert Chagoury, Alhaji Mustapha Indimi da sauransu.

Dangote ya rage farashin man fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar Dangote da ke jihar Legas ta rage farashin da take siyar da kowace litar man fetur.

Matatar ta rage farashin litar fetur daga N890 zuwa N825 wanda zai fara aiki daga ranar Alhamis, 27 ga watan Fabrairun 2025.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng