Sojojin Amurka da Dama Sun Jikkata bayan Hare Haren da Iran Ta kai Masu

Sojojin Amurka da Dama Sun Jikkata bayan Hare Haren da Iran Ta kai Masu

  • Rahotanni sun nuna cewa hare-haren Iran sun jikkata sojojin Amurka da dama bayan kai wa sansanonin soji biyu hari a Jordan
  • Babu rahoton mutuwa, amma an nuna cewa adadin sojojin Amurka da suka jikkata tun bayan fara yaƙin da Iran ya haura 400
  • Iran da Amurka na ci gaba da musayar hare-hare duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a watan da ya gabata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amman, Jordan – Rahotanni sun bayyana cewa wasu hare-haren da Iran ta kai kan sansanonin sojin Amurka a Jordan sun jikkata sojojin Amurka da dama a cikin wannan makon.

Wani rahoto ya nuna cewa an kai hare-haren ne kan aƙalla sansanonin soji biyu da ke Jordan, inda aka tabbatar da jikkatar wasu jami'an sojin Amurka bayan an kai wa cibiyoyinsu hari.

Kara karanta wannan

Masanin da ya yi tsayuwar daka yana kare Musulunci a Amurka ya rasu

Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei
Mojtaba Khamenei a hagu da wani jirgin yaki a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Al Jazeera ta wallafa cewa har yanzu ba a bayyana adadin waɗanda suka jikkata ko irin raunukan da suka samu ba, yayin da Amurka da Jordan suka tabbatar da cewa babu wanda ya mutu sakamakon hare-haren.

An jikkata sojojin kasar Amurka

Rahotanni sun nuna cewa adadin sojojin Amurka da suka mutu tun bayan fara yaƙin da Iran ya kai 14, bayan rasuwar wani matukin jirgin ruwan yaki na rundunar ruwa da ya yi hatsari a farkon watan nan.

Rahoton da the Hill ta wallafa ya bayyana cewa fiye da sojojin Amurka 400 sun samu raunuka tun bayan barkewar rikicin Iran da Amurka.

Iran ta ƙara kai hare-haren jiragen marasa matuƙa da makamai masu linzami kan ƙasashen da ke kawance da Amurka a yankin Tekun Fasha, bayan da Washington ta ci gaba da kai hare-hare kan wuraren sojin Iran na kwanaki da dama a jere.

Tsagaita wuta na fuskantar barazana

Kara karanta wannan

Mutane sun kone kurmus da motar gas ta fashe a kusa da sojoji

Yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran da Amurka suka cimma a watan da ya gabata na ci gaba da fuskantar barazana bayan tattaunawar zaman lafiya ta gaza samun ci gaba.

Amurka ta zargi Iran da kai hare-hare kan jiragen kasuwanci a mashigar Hormuz, yayin da ita kuma Iran ta ci gaba da mayar da martani ta hanyar kai hare-hare kan ƙawayen Amurka da suka haɗa da Jordan, Qatar, Bahrain da Kuwait.

Shugaba Donald Trump
Daonld Trump yana magana a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Mai ba Jagoran Ƙolin Iran, Mojtaba Khamenei, shawara kan harkokin soji, Mohsen Rezaei, ya yi gargaɗin cewa Iran za ta ƙaddamar da "babban farmaki" idan gwamnatin Shugaba Donald Trump ta ci gaba da kai hare-haren makamai masu linzami.

A ranar Juma'a ma, Amurka ta sake kai wani sabon farmaki kan Iran, karo na bakwai a jere, inda jami'an Amurka suka ce manufar hare-haren ita ce rage ƙarfin sojin Tehran.

JD Vance ya zargi Isra'ila

A wani labarin, mun ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya zargi wasu mambobin gwamnatin Isra'ila da ƙoƙarin amfani da ra'ayin jama'ar Amurka domin tsawaita yaƙin da ake yi da Iran.

Kara karanta wannan

'Yan Arewa za su amfana da Amurka ta kawo tallafi mai kyau a fannoni 3 a Najeriya

Rahoton Legit Hausa ya nuna cewa Vance ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da fitaccen mai gabatar da shirye-shiryen podcast, Joe Rogan.

A bayanan da ya yi, mataimakin shugaban kasar ya ce wasu a gwamnatin Isra'ila na ƙoƙarin hana cimma yarjejeniya da Iran ta hanyar tasiri a ra'ayin jama'ar Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng