Kwankwasiyya
Abdulaziz Abdullahi Umar Ganduje ya je ofishin NNPP, ana tunanin zai koma jam’iyya mai kayan marmari. Shi kuwa ‘Danuwansa watau Umar Abdullahi Ganduje 'dan APC ne.
Murja Kunya ta fahimci Hukumar Hisbah ta na kokarin yi mata aure ne, ita kuma ta nuna zama gidan miji zai yi wahala domin manya-manyan bakaken aljanu ne a jikinta.
A karshen zaman SEC da aka yi, Gwamnatin jihar Kano ta amince ayi wasu ayyukan more rayuwa da cigaban al’umma a karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf.
Akinlolu Olujinmi (SAN) ya tsayawa Nasiru Yusuf Gawuna a kotun daukaka kara. Tsohon ministan shari'a ya zama babban lauyan Nasiru Gawuna a shari'ar zaben Kano
Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Rabi'u Yusuf Takai na jam'iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben Majalisar Tarayya a mazabar Takai/Sumaila a Kano.
Kungiyar IPAC ta shawarci Gwamna Abba Kabir yadda zai inganta harkar dimukradiyya a jihar wurin bai wa dukkan sauran 'yan jam'iyyu mukamai a gwamnatinsa.
Lauyoyi sun fito da kuskuren da Kotu ta yi wajen rusa nasarar Abba Gida Gida. Hukuncin da aka zartar a shari’ar zaben shugaban kasa zai raba gardama a jihar Kano.
Gwamna Abba Kabir ya amince da karin girma ga wasu ma'aikata har guda 231 a ma'aikatun jihar Kano daban-daban, ya umarce su da yin aiki tukuru da gaskiya.
Kotun Tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta dakatar da Gwamna Abba Kabir Yusuf kan matakin da ya dauka kan makarantu ma su zaman kansu a jihar Kano.
Kwankwasiyya
Samu kari