Zaben Majalisa: Tsohon Gwamnan Arewa Mai Yakar APC Ya Yi Kus-Kus da Kwankwaso

Zaben Majalisa: Tsohon Gwamnan Arewa Mai Yakar APC Ya Yi Kus-Kus da Kwankwaso

  • Abdul'aziz Yari ya je gidan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, sun yi wata tattauna da ta shafi siyasa
  • Babu mamaki zababben Sanatan yana neman goyon bayan jagoran jam'iyyar NNPP a Majalisa
  • Jam’iyyar NNPP ta na da zababbun Sanatoci da za su iya taimakon Yari a takarar majalisar dattawa

Abuja - Abdul'aziz Yari yana cikin wadanda su ka dage a neman shugabancin majalisar dattawa, duk da jam’iyyar APC ta ayyana 'yan takara.

Ana haka sai ga hotuna a shafin Twitter cewa Alhaji Abdul'aziz Yari ya yi zama da jagoran jam’iyyar NNPP a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso.

Tsohon Gwamnan na Zamfara ya kebe da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a gidan ‘dan takaran shugaban kasar da ke babban birnin tarayya Abuja.

Gidan Kwankwaso
Abdulaziz Yari, Rabiu Kwankwaso da Kawu Sumaila Hoto: @SaifullahiHassan
Asali: Twitter

Baya ga kebewa da ya yi da tsohon Gwamnan na Kano, Yari ya zauna da zababbun Sanatocin Kano na jam’iyyar NNPP a Maitama a yammacin yau.

Kara karanta wannan

Daf da Zai Bar Mulkin Najeriya, Buhari Ya Amince a Kafa Sabuwar Jami'ar Tarayya

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda hotunan da aka fitar a shafin gidan rediyon Nasara FM su ka nuna, an ga Rufai Hanga da Abdulrahman Kawu Sumaila a wajen zaman.

Haka zalika Legit.ng ta fahimci Injiniya Buba Galadima, wanda yana cikin jiga-jigan jam’iyyar adawa ta NNPP, ya samu halartar tattaunawar da aka yi.

Hadimin ‘dan siyasar, Saifullahi Hassan ya fitar da hotunan wannan zama da aka yi, amma bai fadi dalilin ziyarar da aka kai wa mai gidan na sa ba.

Babu matsaya tukuna - Hanga

Ana haka sai aka labari Sanata Rufai Hanga wanda zai wakilci Kano ta tsakiya ya na cewa NNPP ba ta kai ga tsaida wadanda za ta marawa baya ba.

Hanga ya ce da jam’iyyarsu ke da rinjaye, da tuni su tsaida ‘yan takaransu, amma yanzu su na zama kuma su na sauraron dukkanin 'yan takaran.

Kara karanta wannan

Barazanar Sanatocin Jihohin Arewa Ya Jawo APC Ta Ji Uwar Bari a Kan Takarar Majalisa

Kano za ta amfana da Majalisa ta 10?

Babban ‘dan siyasar ya tabbatar da cewa sun ajiye sabanin jam’iyya a gefe, sun hadu da Sanatoci har da na APC irinsu Barau Jibrin domin cigaban Kano.

A dalilin haka Hanga ya dage Abdulrahman Kawu Sumaila ya samu mukami domin ya taba shugabanci a majalisar wakilai kuma an yarda da kwazonsa.

Sanatan ya ce Rabiu Kwankwaso ya ba su umarni su dage ka da a maida Kano a baya. Idan aka yi dace, Sumaila zai samu kujera ta marasa rinjaye.

Za a yaki Akpabio/Jibrin

A rahotonmu, kun ji masu harin kujerar Ahmad Lawan sun nuna za su yi fito na fito da jam’iyyarsu a dalilin tsaida Godswill Akpabio da Barau Jibrin.

Shugaban Jam’iyyar APC ya zauna da Orji Kalu, Sani Musa, da Abdulaziz Yari domin ya lallashe su, Osita Izunaso bai samu zuwa wajen taron na jiya ba.

Kara karanta wannan

Yari da Wasu Fusatattun Sanatoci 3 Masu Neman Shugabancin Majalisa Sun Yi Kus-Kus da Shugabannin APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel