Abubuwa 2 Rak Za Su Hana Abba Kabir Yusuf Zama Gwamnan jihar Kano – Jagoran APC

Abubuwa 2 Rak Za Su Hana Abba Kabir Yusuf Zama Gwamnan jihar Kano – Jagoran APC

  • Ahmadu Haruna Dan Zago yana ganin yaudarar kai ne cewa jam’iyyar APC za ta zarce a Jihar Kano
  • Duk da yana cikin ‘yan jam’iyyar APC, ‘dan siyasar ya ce da wahala a fasa rantsar da Abba Kabir Yusuf
  • Ambasada Dan Zago ya ce mutuwa ko yi juyin mulki kadai ne za su hana NNPP kafa Gwamnati a 2023

Kano - Ahmadu Haruna Dan Zago wanda yana cikin jagororin jam’iyyar APC a jihar Kano, ya fadakar da mutanensa da cewa su zama wayayyu.

A wata zantawa da ya yi da gidan rediyon Nasara FM, ‘dan siyasar ya ce yaudarar kai ne kurum a rika tunanin APC za ta zarce a kan mulki a Kano.

Ambasada Ahmadu Haruna Dan Zago ya nuna babu ta yadda za a fasa rantsar da Abba Kabir Yusuf, a nada Nasiru Yusuf Gawuna a madadinsa.

Kara karanta wannan

Barazanar Sanatocin Jihohin Arewa Ya Jawo APC Ta Ji Uwar Bari a Kan Takarar Majalisa

Abba Gida Gida
Abba Gida Gida ya karbi shaidar nasara Hoto: @Noble_Hassan
Asali: Twitter

A matsayinsa na gogagge, Dan Zago ya ce ana neman maida ‘ya ‘yan APC jahilai, wawaye ko dakikai, har ma yana neman zama masu abin kunya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jagoran na APC yake cewa dokar kasar nan da tsarin mulki sun ce bayan kwanaki bakwai da ayyana zabe, duk wanda bai gamsu ba ya garzaya kotu.

An rahoto Dan Zago yana cewa in dai ba kotun koli ta ruguza nasarar jam’iyyar NNPP, babu yadda za a warware rantsar da Abba Kabir Yusuf da za ayi.

Me zai hana rantsar da Abba?

Tun da an yi zabe, kuma an bada takardar shaidar nasara, ana jiran rantsuwa, mu na da hankali, mu ba jahilai ba ne.
Abin da za su hana a rantsar da Abba a Kano; Ko dai ya mutu ko kuma an yi juyin mulki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Abin da ‘Yan Takaran Kujerun Majalisa Su ka Fadawa Shugaban Jam’iyyar APC Gar da Gar

Idan Allah ya karbi kwanansa, dama ‘Dan Adam ne shi kuma duk mai rai mamaci. Ko kuma juyin mulki aka yi a Najeriya, aka jingine tsarin mulkin.
Amma ina tabbatar maka ba a yin Kantoma a gwamna. Sai dai idan an kafa gwamnatin riko na gaggawa, ita ma watanni shida ta ke ciki.
Amma idan an yi zabe babu wata karya da za ayi wa mutane cewa ba za a rantsar da shi ba.

- Ahmadu Haruna Dan Zago

Su wanene ke cewa za a rantsar da Gawuna?

Duk wanda ya fadi haka dayan biyu ne ko dai hankalinsa ba cikakke ba ne ko kuma ba shi da ilmin zamani da na addini da sanin rayuwa.

A cewar ‘dan siyasar, na ukun da zai ce Nasiru Gawuna zai gaji Abdullahi Ganduje shi ne wanda bai san abin da ake kira da damukaradiyya ba.

Hira da Layan NNPP

Bashir Yusuf Muhammad Tudun Wazirci ya yi karin haske a kan shari’ar zaben Kano, an ji labari ya yi kaca-kaca da masu wannan tunani.

Lauyan ya fada mana tun farko Jam’iyyar APC tayi kuskure wajen shigar da kara a kotun zabe, ya ce tamkar Abba Yusuf ya dare kan mulki ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel