Mai Magana da Yawun Bakin Kwankwaso a Zabe, Ya Je Gida, Ya Kebe da Bola Tinubu

Mai Magana da Yawun Bakin Kwankwaso a Zabe, Ya Je Gida, Ya Kebe da Bola Tinubu

  • Abdulmumin Jibrin ya kai ziyara ta musamman zuwa wajen Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a Abuja
  • Zababben ‘dan majalisar wakilan na Jam’iyyar NNPP ya yi zama da zababben shugaban Najeriya
  • Zuwa yanzu babu wanda ya san makasudin ganawar da Jibrin ya yi da Shugaban kasa mai jiran gado

Abuja - Abdulmumin Jibrin ya taka da kafafunsa, ya kai ziyara zuwa gidan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mai shirin zama shugaban Najeriya.

Daya daga cikin Hadiman Gwamnan jihar Legas, Jibril Gawat ya sanar da Duniya wannan ziyara da ya fitar da hoton haduwar a shafin Twitter.

Gawat mai taimakawa Mai girma Babajide Sanwo Olu a kafafen sadarwan zamani ya ce Abdulmumin Jibrin ya tsaya domin ya gaida Bola Tinubu.

Hakan yana zuwa a lokacin da ‘yan siyasa barkatai ke kai-komo a gidan zababben shugaban kasar bayan dawowarsa daga Faransa a makon nan.

Kara karanta wannan

Somin-tabi: Bidiyon lokacin da Tinubu da Shettima ke kaura zuwa gidan gwamnati

Tafiyar Jibrin a zaben 2023

Abdulmumin Jibrin yana cikin wadanda da farko suka taya Bola Tinubu yakin zama shugaban kasa, amma a karshe ya sauya-sheka zuwa NNPP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jibrin ya samu takara kuma ya ci zaben ‘dan majalisar wakilai a jam’iyyar NNPP, kuma ya kasance kakakin Rabiu Kwankwaso wajen kamfe.

Jibrin
Abdulmumin Jibrin da Bola Tinubu Hoto: @Mr_JAGs
Asali: Twitter

‘Dan takaran na APC watau Tinubu ya yi galaba a kan Kwankwaso a zaben shugaban Najeriya, amma NNPP ba ta shigar da kara a kotu ba.

Akwai sauran kallo a siyasa

Ziyarar ta jawo irinsu Injiniya M. S Ingawa su na ganin Hon. Jibrin wanda zai sake wakiltar Kiru/Bebeji zai iya goyon bayan APC a majalisar wakilai.

M. S Ingawa ya ce idan zababben ‘dan majalisar zai samu kwamiti ko wata kujera mai tsoka, ‘yan NNPP za su iya ba APC mai rinjaye goyon baya.

Kara karanta wannan

Zababbun ‘Yan NNPP, LP, da PDP Za Su Goyi Bayan ‘Dan APC a Zaben Majalisar Tarayya

Abdulaziz Na’ibi wanda shi kuma Atiku Abubakar ya marawa baya a zaben 2023, yana zargin tun farko dama jirgi daya ya dauko APC da NNPP.

A lokuta dabam-dabam, ‘dan siyasar ya nuna shi da sauran ‘yan adawa su na da rinjayen da za su iya tasiri wajen tsaida wanda zai rike majalisa.

An kori Jibrin daga FHA

A shekarun baya aka ba Abdulmumin Jibrin kujera a FHA ganin an raba shi daga matsayin da yake kai a Majalisar Wakilan Tarayyan kasar nan.

Bayan ‘yan shekaru, sai aka ji labari Hukumar gidajen ta kori ‘Dan siyasar a sakamakon bincike da aka yi a kan shi na sabawa ka'idar aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel