Bayan Haduwa da Tinubu a Kasar Waje, Kwankwaso da Abba Sun Dura Garin Legas

Bayan Haduwa da Tinubu a Kasar Waje, Kwankwaso da Abba Sun Dura Garin Legas

  • Rabiu Musa Kwankwaso da zababben Gwamnan Kano watau Abba Kabir Yusuf su na garin Legas
  • A halin yanzu ana sa ran shugaban kasa ya kaddamar katafaren matatar da Aliko Dangote ya gina
  • Akwai yiwuwar Gwamnoni da zababben shugaban Najeriya su halarci bikin kaddamar da matatar

Lagos - Jagoran NNPP kuma wanda ya yi wa jam’iyyar takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya shiga garin Legas.

Kamar yadda wani Hadiminsa ya sanar a shafin Twitter, Rabiu Musa Kwankwaso ya isa Legas ne a ranar 21 ga watan Mayun 2023.

Saifullahi Hassan ya ce Rabiu Kwankwaso yana tare ne da zababben Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a wajen wannan tafiya.

Kwankwaso da Abba
Rabiu Musa Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf a Legas Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter
"Jagoran @OfficialNNPPng na kasa, Mai girma Sen. @KwankwasoRM (Rabiu Musa Kwankwaso) tare da zababben Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a yau (jiya), 21 ga watan Mayu 2023

Kara karanta wannan

Ba A Je Ko Ina Ba, An Fara Zargin Gwamnan APC Da Yakar Gwamna Mai Jiran Gado

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun iso babban filin tashi da saukar jirgin sama na Murtala Muhammad da yake garin Legas."

- Saifullahi Hassan

Mun fahimci tsohon Gwamnan na jihar Kano ya je Legas ne domin ya halarci bikin kaddamar da katafaren matatar Aliko Dangote.

Matatar Aliko Dangote

Mutumin Kano kuma shahararrren ‘dan kasuwar nan, Alhaji Dangote ya gina matatar da za ta iya tace ganguna 650, 000 a rana.

Punch ta ce kamfanin zai taimaka wajen yin hanyar da mutane 100, 000 za su samu aiki, kuma ya jawowa Najeriya $21bn a shekara.

Shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da katafaren kamfanin a safiyar Litinin.

Ana sa ran an gayyaci manyan mutane daga ciki har da Gwamnoni, hakan ya na nufin za a iya ganin Abdullahi Umar Ganduje.

Daily Trust ta ce shugabannin kasashe shida za su halarci wannan biki, sun hada da na: Togo, Ghana, Chad, Sanagal da na kasar Nijar.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Amince da Rabon Sababbin Mukamai a Hukumar FERMA

Watakila a ga Ganduje

Akwai yiwuwar wannan bikin kaddamarwa ya hada zababben shugaban kasa watau Bola Tinubu da Kwankwaso da magajin na sa.

Hakan ya na zuwa ne yayin da rahotanni ke yawo Gwamna Abdullahi Ganduje bai dadin zaman da Tinubu ya yi da Kwankwaso ba.

Daga ganin hotunan har wasu sun fara tofa albarkacin bakinsu a dandalin Twitter.

Muhammad Gambo Ibrahim yake tambaya:

“Za a kuma wata ganawar sirri ne”

Umar Farouk Injay ya ce:

“Shugaban gobe da yardar Allah.”

Tinubu zai karbi kasa

Ku na da labari Bola Tinubu da Kashim Shettima za su karbi mulkin Najeriya, akwai bashin N77tr da manya-manyan ayyuka a gabansu.

Gwamnatin da za ta gaji shugabanci a farkon makon gobe ta na da danyen aiki a gabanta tun daga tattalin arziki zuwa ilmi da kiwon lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel