Kwankwaso Ya Duro Najeriya, Ana Jiran Ya Fadi Yadda Suka Yi da Tinubu a Faransa

Kwankwaso Ya Duro Najeriya, Ana Jiran Ya Fadi Yadda Suka Yi da Tinubu a Faransa

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya shigo Najeriya bayan wata gajerar tafiya da ta kama shi zuwa Faransa
  • A yayin da ya ke Turai, ‘dan siyasar ya yi zaman sirri da zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu
  • Sanata Kwankwaso ya yi alkawari yau ne zai fadawa Duniya abin da ya tattauna da Tinubu a Faris

Abuja - ‘Dan takaran shugaban kasa a zaben da ya gabata a Najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso ya iso Najeriya bayan kwanaki a kasar waje.

Da kimanin karfe 10:30 na daren ranar Laraba, 18 ga watan Mayu 2023 aka tabbatar da shigowar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Najeriya.

Saifullahi Hassan wanda Hadimin tsohon Gwamnan na Kano ne ya wallafa hotunan saukar Mai gidansa a filin jirgin sama da ke garin Abuja.

Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankaso a filin jirgi Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Tawagar Madugun Kwankwasiyya

Kara karanta wannan

Bayanai Sun Cigaba da Fitowa Kan Mutanen da Tinubu Zai Ba Mukamai a Gwamnati

A cikin wadanda suka tarbo Rabiu Kwankwaso akwai abokin gaminsa a zaben 2023, Bishof Isaac Idahosa da wasu jagororin jam’iyyar NNPP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng Hausa ta fahimci har da Mashood Shittu da Ibrahim Adam aka yi wa Kwankwaso maraba a filin tashi jirgi na Nnamdi Azikiwe.

Kafin zuwansa kasar Faransa, Kwankwaso ya je Kano inda ya kai ziyara zuwa wurare, ya yi ta’aziyya a gidajen manyan da aka yi rasuwa.

Daga Abuja zai Faris

Daga nan mu ke zargin ‘Dan siyasar ya zarce Abuja, a karshen mako ya tafi kasar Faransa, ya hadu da Bola Tinubu da Muhammadu Sanusi.

Ganin karshe da aka yi wa Sanata Kwankwaso a fili shi ne haduwarsa da Abdulaziz Yari a gidansa da ke unguwar Maitama a birnin tarayya Abuja.

A jawabin da ya fitar a Twitter, Saifullahi Hassan ya ce gajerar tafiya mai gidansa ya yi zuwa kasar Turan, amma bai yi wani karin bayani a kai ba.

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Kwankwaso Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Ganawar da Ya Yi da Bola Tinubu a Faransa

Dawowar fitaccen ‘dan siyasar ke da wahala, mutane sun kagara su ji maganar da zai yi a game da ganawar da ya yi da Bola Tinubu a birnin Faris.

Abba ya dawo daga Ingila

Ana haka ne sai aka ji zababbun ‘yan majalisar Kano a karkashin jam’iyyar NNPP sun ziyarci Abba Kabir Yusuf domin yi masa maraba da zuwa.

Gwamna mai jiran gado, Abba Gida-Gida ya dawo daga gida bayan ‘yan kwanaki a Ingila.

Ya aka yi a Faris?

A rahoton da aka fitar a baya, an ji labarin yadda Bola Tinubu ya yi wa Rabiu Musa Kwankwaso tayin kujerun Ministoci biyu a Gwamnatinsa.

Zababben shugaban kasar ya sa labule da tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II, haka zalika shi ma tsohon Gwamnan ya hadu da Mai martaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel