Buba Galadima: Abin da Ya Hana Kwankwaso Zuwa Kotu a Kan Zaben Shugaban Kasa

Buba Galadima: Abin da Ya Hana Kwankwaso Zuwa Kotu a Kan Zaben Shugaban Kasa

  • Buba Galadima ya nuna hakura kurum su ka yi da zuwa kotu, ba saboda ba su hangen nasara ba
  • Jagoran na jam’iyyar NNPP yana ganin shigar da kara a kotun zabe ba zai taimakawa Najeriya ba
  • Injiniya Galadima yana da ra’ayin Tinubu ba zai kai labari muddin NNPP ta kalubalanci zaben 2023

Abuja - Buba Galadima wanda yana cikin jagororin jam’iyyar NNPP a kasar nan, ya yi bayanin abin da ya hana su zuwa kotu a kan zaben shugaban kasa.

A hirar da aka yi da shi a tashar Arise TV, Injiniya Buba Galadima ya ce ba su je kotu su kalubalanci nasarar Bola Tinubu ba ne saboda dole Najeriya ta cigaba.

‘Dan siyasar ya yi ikirarin ba su sha’awar lalata zaben nan da aka yi, saboda haka su ka yi hakuri.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya Bada Muhimman Shawarwari 4 da Za su Iya Taimakon Bola Tinubu a Mulki

Idan da jam’iyyar NNPP ta tafi kotu, Buba Galadima ya shaidawa manema labarai cewa hakan zai bada dama wasu su nemi a kafa gwamnatin rikon kwarya.

NNPP za ta yi nasara a kotu

Rabiu Musa Kwankwaso ya zo na hudu ne a zaben sabon shugaban Najeriya, duk da haka daya daga cikin kusoshin NNPP a kasar yana ganin cin ta a gaban kotu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Atiku Abubakar da Peter Obi su na shari’a da Bola Tinubu da APC a kan makomar zaben, shi kuwa Sanaa Kwankwaso bai nuna ya damu da sakamakon zaben ba.

Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso a yakin zaben Shugaban Kasa Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

"Na fada, idan da akwai wani wanda zai je kotun zabe, kuma ya yi nasara wajen kalubalantar jam’iyyar APC, NNPP ce.
Na farko saboda ba a daura sunan jam’iyyar NNPP a takardar kada kuri’u ba, kuma wannan kadai ya isa a soke zaben nan.

Kara karanta wannan

"Na Yi Nadamar Mulkin Buhari Saboda Manyan Abu 2 da Ya Kawo" Tsohon Makusancin Buhari Ya Tona Asiri

Sannan ba gane takenmu ba, baya ga haka kuri’un da aka saba kadawa miliyan 32 ne, wannan karo ba su kai miliyan 20 ba.
Zarginmu shi ne an samu raguwar adadin masu zabe ne saboda wadanda za su kadawa Kwankwaso ba su ga jam’iyyarsa ba."

- Buba Galadima

Abubuwa sun tabarbare a yau

The Cable ta rahoto Injiniyan yana cewa zuwa kotu ba zai taimaki kowa ba, dole a bada dama domin kasa ta samu cigaba, a rufe kofar kafa gwamnatin riko.

A hirar ne kuma ‘dan siyasar ya karyata Femi Adesina, ya ce Muhammadu Buhari ya jagwalgwala abubuwa a Najeriya, abubuwa sun lalace a yau fiye da a 2015.

Bikin ranar ma'aikata

A wani rahoto da aka fitar a baya, an ji Shugaban Najeriya mai haramar barin gado ya ba Bola Tinubu shawarar ya kula da ‘yan kwadago idan ya shiga ofis.

Muhammadu Buhari yana so ma’aikata su ci moriyar gwamnatin tarayya. A jawabinsa, Tinubu ya nuna ba zai manta da ma'aikata a mulkinsa ba.

Kara karanta wannan

Toh fa: Tinubu ya watsar da 'yan APC, ya ce ba dan wani gwamnan PDP ba da ya fadi zabe

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng