Gaskiyar Bayanan Zaman Kwankwaso, Tinubu, da Sanusi a Faransa Sun Fara Bullowa

Gaskiyar Bayanan Zaman Kwankwaso, Tinubu, da Sanusi a Faransa Sun Fara Bullowa

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya dauki lokaci ya na ganawar sirri da Asiwaju Bola Tinubu a kasar Faransa
  • An yi wani zama dabam tsakanin zababben shugaban Najeriya da Mai martaba Muhammadu Sanusi II
  • Akwai masu sa ran Khalifa Sanusi zai koma gadon sarauta, wasu su na so a ba shi kujera ne a gwamnati

France - Bayanai su na kara fitowa fili a kan haduwar da zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya yi da Rabiu Musa Kwankwaso a birnin Faris.

Baya ga kus-kus da ya yi da Bola Tinubu, tsohon Gwamnan na jihar Kano ya zauna da Muhammadu Sanusi II, Daily Trust ta tabbatar da hakan a safiyar nan.

Majiya ta tabbatar da cewa Kwankwaso ya zanta da shugaban kasa mai jiran gado, sannan kuma ya hadu da Mai martaba Sarkin Kano na 14 a kasar wajen.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Fadi Abin da Zai Faru Idan Kwankwaso Ya Shigo Gwamnatin Tinubu

Kwankwaso, Tinubu, da Sanusi
Rabiu Musa Kwankwaso da Muhammadu Sanusi Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Idan rahoton ya tabbata, an yi wani zama na uku tsakanin Bola Tinubu wanda zai karbi mulkin Najeriya da Khalifan Tijjaniya, Muhammadu Sanusi II.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta ce makasudin tattaunawar da aka yi shi ne shugaban mai jiran-gadon ya samu alaka mai kyau tsakaninsa da wadannan fitattun mutanen Kano.

A yayin da ake yi wa Rabiu Kwankwaso kallon ‘dan siyasa mai farin jini musamman a Arewa, Sanusi II mutum ne mai ilmin zamani wanda ya san kan aiki.

Da Kwankwaso ya sa labule da shugaba mai jiran gadon, ya fada masa ya yi shawara da mutanensa kan yiwuwar su hada-kai su yi aiki tare a gwamnatinsa.

Jaridar ta ce ‘yan siyasar sun amince za su sake ganawa bayan nan. Kafin haka ya yi masa tayin ya zabi kujerar Ministan ilmi ko kuwa Ministan harkar gona.

Kara karanta wannan

Kwanaki 13 Kafin Ya Bar Aso Villa, Buhari Ya Fadi Kokari 3 da Ya Yi Cikin Shekaru 8

Babu tabbacin ko Kwankwaso zai karbi wannan tayi ko zai bada kujerar ne ga yaransa a siyasa. Legit.ng Hausa ta fahimci zai yi magana a ranar Alhamis.

Kwankwaso ya zauna da Sanusi

A gefe guda kuwa, ba a samu cikakken bayanin abin da ya wakana a yayin da Sanata Kwankwaso ya zauna da Muhammadu Sanusi a kasar nahiyar Turan ba.

Hotuna su na yawo tun farkon makon nan a daidai lokacin da ake cigaba da rade-radin Gwamnatin Abba Yusuf za ta cire Aminu Ado Bayero daga kan karaga.

Nadin Tinubu yana tangal-tangal?

Rahoto ya zo cewa an kuma samun wani Lauya da ya shigar da sabuwar kara a kan Bola Tinubu a kotun Abuja a madadin kungiyar ASRADI a makon nan.

ASRADI ta na so a hana Bola Tinubu jin kanshin Aso Villa, ta ce zababben shugaban kasar ya yi wa hukumar INEC karya, don haka bai dace ya hau mulki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel