Hadimin Buhari Ya Fadi Abin da Zai Faru Idan Kwankwaso Ya Shigo Gwamnatin Tinubu

Hadimin Buhari Ya Fadi Abin da Zai Faru Idan Kwankwaso Ya Shigo Gwamnatin Tinubu

  • Bashir Ahmaad ya fito fili ya nuna za su so a ce Rabi'u Musa Kwankwaso ya shigo tafiyarsu a APC
  • Mai taimakawa shugaban Najeriya a kafofin sadarwa na zamani ya na ganin muhimmancin ‘dan siyasar
  • Hadimin shugaban kasar ya ce za su karbi tsohon ‘dan takaran shugaban kasar idan ya sauya-sheka

Paris - Rahotanni su na ta yawo ta ko ina cewa Rabi'u Musa Kwankwaso ya zanta da Bola Ahmed Tinubu a birnin Paris a kasar Faransa kwanan nan.

Hakan ya jawo wasu mutane su ke ta tofa albarkacin bakinsu a game da juyin da zai iya canza siyasar Arewacin Najeriya musamman kuwa jihar Kano.

Bashir Ahmaad wanda yana cikin mukarraban shugaba mai barin-gado, Muhammadu Buhari, ya goyi bayan APC ta jawo Rabiu Musa Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Gwamnan Jihar Taraba Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Fitar Da N2bn a Asusun Jihar Domin Siyo Motocin Kece Raini

Kwankwaso
Kwankwaso a lokacin ya na APC Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Da yake magana a Twitter a ranar Talata, Bashir Ahmaad ya nuna Rabiu Kwankwaso zai yi wa zaɓaɓɓen shugaban na Najeriya amfani a gwamnatinsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Shakka babu, mu na bukatar Kwankwaso a jam’iyyarmu a Kano. Za mu yi farin cikin sake karbar shi."

- Bashir Ahmaad

Yakubu Aminu Usman ya tunawa ‘Yan Gandujiyya wata magana da ya taba yi a Twitter, ya yi hasashen cewa Madugun na Kwankwasiyya zai shigo APC.

"Ko ina za a je mun shirya"

A shafinsa na Facebook, Salisu Yahaya Hotoro wanda yana cikin ‘yan gani-kashenin Kwankwaso ya ce sun shirya bin jagoran na su zuwa duk inda ya tsunduma.

Hotoro ya yi wa Bola Tinubu godiya na tayin da ake tunanin ya yi wa jigon na NNPP, ya ce ba za su ci amana ba, har aka ga ya fara yabon shugaba mai jiran-gado.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamna Ya Ba Tinubu Shawarwarin Abubuwan da Zai Yi Idan Ya Hau Kan Mulki

“Tinubu mun gode kuma Insha Allah zaka san kayi da ƴan halak. Za mu saka halacci da halacci.
Tafiya ta Kwankwaso ko ina za’a je mun shirya.

- Salisu Yahaya Hotoro

'Yan Atiku sun fusata

Shi kuwa Abdulaziz Na’ibi Abubakar ya soki ‘dan takaran na 2023, ya ce tun farko Kwankwaso bai bar APC ba, ya yi amfani da NNPP ne domin cin zaben Kano.

Masoyin na Atiku Abubakar ya zargi ‘dan adawar da cin amanar PDP a zaben 2019, sannan ya ce da shi da Nyesom Wike APC tayi amfani wajen cin zaben bana.

Abin ayi murna ne

Hassan Sani Tukur ya na cikin matasan Kwankwasiyya, ya shaidawa Legit.ng Hausa haka su ke ganin labari yana yawo cewa Bola Tinubu ya yi masu tayi.

A tsarin Kwankwasiyya, Hassan Tukur ya ce idan magana irin haka ta taso, dole za nemi ta-cewar jagorori, yake cewa a kullum su masu yin biyayya ne.

Matashin ya ce shi da ire-irensa su na farin ciki da wannan lamari musamman ganin NNPP tayi wa APC hamayya, ya ce hakan ya nuna an san darajarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel