Kasar Saudiya
Maniyyatan Najeriya sun shiga cikin halin rashin tabbas yayin da kungiyoyin kwadago suka fara yajin aiki. An hana jirage jigilar maniyyatan zuwa Saudiyya.
Ronaldo ya zubar da hawaye bayan da kungiyarsa ta Al Nassr ta sha kashi a hannun Al Hilal a bugun fanariti a wasan karshe na gasar cin kofin sarki a ranar Juma'a.
Gwamnatin jihar Yobe karkashin Mai Mala Buni ta tabbatar da biyan kuɗin da ta yiwa alhazan jigar alkawari, an kamma kwashe su zuwa ƙasa mai tsarki.
Hukumar NAHCON ta bukaci maniyyatan Najeriya da suka isa Makkah da su nemi taimakon likitoci daga duk wani asibitin gwamnatin Saudiyya idan bukatar hakan ta taso.
Hukumar alhazai ta Najeriya (NAHCON) ta gargadi maniyyata aikin hajjin 2024 da su guji tafiya Saudiya da haramtattun kayayyaki, irin su kwayoyi, sigari da goro.
Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Legas ta tabbatar da rasuwar ɗaya daga cikin alhazan jihar, Idris Oloshogbo, wanda ya rasu bayan dawowa daga Ɗawafi a Makkah.
Wani Alhaji daga Kebbi ya rasu bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya a birnin Makka na kasar Saudiyya. An yi sallar jana’izarsa a masallacin Harami (Ka’aba).
Wata maniyyaciya daga jihar Kebbi ta rasu a birnin Makka da ke kasar Saudiyya a ranar Asabar 25 ga watan Mayu bayan ta sha fama da gajeruwar jinya na wani lokaci.
A yayin da duniya ke jimamin mutuwar shugaban Iran, Ebrahim Raisi, a hannu daya kuma, an kwantar da sarkin Saudiya, Salman bin Abdulaziz a asibiti saboda cutar huhu.
Kasar Saudiya
Samu kari