Jirgin Sama
Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma jagoran jam'iyyar LP, Peter Obi ya bada labarin yadda ya cire girman kai ya wanke bandakin jirgin sama a shekarun baya.
An samu jirgin saman Air India bayan shekara 13 ba a same shi ba. An samu jirgin ne a wani filin jirgin sama kuma an sayar da shi bayan biyan harajin da ake nema.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tashi daga Abuja zuwa Borno, Bauchi da Lagos, inda zai ƙaddamar da ayyuka, yin ta’aziyya da kuma hutun bikin Kirsimeti.
Wani jirgin sama na masu kudi da ya taso daga Kaduna ya yi hatsari a filin jirgin Owerri bayan ya samu matsala a sararin samaniya, NSIB ta ce babu asarar rai.
Wani jirgin sama dauke da fasinjoji ya gamu da hatsari a filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu Kano. An yi kokarin ceto mutanen da ke cikinsa.
Shugabannin kasashen AES da suka hada da Mali, Nijar, Burkina Faso sun bayyana cewa za su harbo duk wani jirgin da ya keta sararin samaniyarsu bayan rike na Najeriya
Sojojin Najeriya biyu sun tsira lafiya bayan sun yi hatsari a jihar Niger wanda ya faru da jirgin, bayan matsala da ta taso jim kaɗan da tashin jirgin a Kainji.
Rahotanni daga jihar Neja sun nuna cewa wani jirgin sama da rundunar sojin saman Najeriya ya gamu da hatsari da yammacin yau Asabar, babu wanda ya rasa ransa.
A labarin nan, za a ji cewa jirgin saman gwamantin Najeriya da aka saka a kasuwa kimanin watanni biyar da suka gabata ya yi kwantai, an janye shi daga kasuwa.
Jirgin Sama
Samu kari