Jirgin Sama
Jirgin saman kamfanin Air Peace ya yi wata saukar gaggawa bayan samun matsala a sama. Jirgin ya dauko mutane daga Benin na jihar Edo zuwa birnin Abuja.
Ofishin binciken tsaron Najeriya (NSIB) ya sanar da gano karin gawar mutum guda da hatsarin jirgin sama ya rutsa da su da jihar Ribas. Hadarin ya afku a makon jiya.
Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta maincewa Gwamna Usman Ododo ya gina katafaren filin sauka da tashin jiragen sama na kasa da kasa a Zariagi, jihar Kogi.
Shugaba Bola Tinubu ya nemi a tsaurara bincike da aikin ceto yayin da ake fargabar fasinjoji takwas sun mutu a hatsarin jirgin sama da ya faru a jihar Ribas.
An samu bayanai kan matukin jirgin saman da ya yi hadari da jami'an NNPCL. Wanda haɗarin ya ritsa da shi babban ne sosai a kungiyar matuƙa jirgin sama ta kasa.
Mai magana da yawun kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye ya tabbatar da cewa jirgin mai saukar ungulu da ya yi hatsari a Ribas mallakin kamfanin East Winds ne.
Mutane uku sun rasa rayukansu bayan jirgi mai saukar ungulu ta fadi a birnin Port Harcourt da ke jihar Rivers inda mutane uku suka rasa rayukansu dalilin haka.
Rundunar sojin saman Najeriya za ta samu sababbin jiragen yaki 50 domin cigaba da kai hare hare kan yan bindiga. Sojoji za su cigaba da luguden wuta kan yan ta'adda.
Gwamnatin tarayya ta kara tabbatar da cewa za ta fatattaki yan ta'adda da su ka hana jama'a zaman lafiya, musamman a yankin Arewa maso Yammacin kasar nan.
Jirgin Sama
Samu kari