Ibadan
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde,ya nemi amincewar majalisar dokokin jihar domin ciyo bashin Naira biliyan 150 daga cibiyoyin hada-hadar kudi na Afrexim da Access.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana dalilin tashin abin fashewa a birnin Ibadan a jihar Oyo. Gwamnan ya ce laifin masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba ne.
Al'ummar garin Ibadan sun shiga zullumi sakamakon kara da girgiza da aka ji biyo bayan tashin wani abin fashewa da wasu ke zargin tukunyar gas ne ko bam.
Manyan masu fada aji daga bangarori daban-daban suna ta isa cibiyar taro ta jami’ar Ibadan, inda ake bikin cikar jigon APC, Cif Akande shekaru 85.
Babban malamin Musulunci a jihar Oyo, Sheikh Abdulfatai Muhali Alaga ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 80 a duniya a yau Talata a Ibadan.
Mazauna garin Ibadan na jihar Oyo, sun bayyana jin dadinsu bayan da suka samu ruwan sama na farko a shekarar 2024, a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairu.
Gwamna Seyi Makinde ya sha alwashin ba zai biya ko sisi ga tsaffin ciyamomin kananan hukumomin jihar ba da ya kora har sai Kotun Koli ta umarce shi.
Hukumar kiyaye haɗurra reshen jihar Ogun ta tabbatar da mutuwar fasinjoji 10 a wani mummunan hatsari da ya auku da asubahin ranar Talata, 12 ga watan Disamba.
Kotu da dakatar da Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun kan shirinsa na korar shugabar alkalan jihar, Mai Shari'a, Oyebola Ojo daga mukaminta a jihar.
Ibadan
Samu kari