Gwamnan PDP Ya Rufe Wurin Ibada Kan Damun Jama’a da Kara, Ya Gargadi Mutane Kan Saba Dokar

Gwamnan PDP Ya Rufe Wurin Ibada Kan Damun Jama’a da Kara, Ya Gargadi Mutane Kan Saba Dokar

  • Gwamnatin jihar Oyo ta gargadi wuraren ibada da kasuwanni da kuma kamfanoni kan damun jama’a da kara
  • Wannan na zuwa ne bayan ta rufe wani coci a unguwar Golden da ke Oluyole a birnin Ibadan da ke jihar
  • Wannan mataki an dauke shi ne bayan kokarin samun maslaha amma abin ya ci tura tsakanin mazauna yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo – Gwamnatin jihar Oyo ta umarci kulle wani coci kan yadda suke damun jama’a da kara.

An kulle cocin New Generation ne da ke Unguwar Golden a Oluyole da ke Ibadan a jiya Alhamis 1 ga watan Faburairu.

Gwamnan PDP ya rufe wurin ibada kan wasu dalilai
Gwamna Makinde ya rufe wani coci saboda damun jama'a da kara. Hoto: Seyi Makinde, New Generation Church.
Asali: Facebook

Wane mataki gwamnatin Oyo ta dauka?

Kara karanta wannan

Majalisar jihar PDP ta bukaci cafke shugaban Fulani kan wasu dalilai 2, ta bayyana zarge-zargen

Wannan mataki an dauke shi ne bayan kokarin samun maslaha amma abin ya ci tura tsakanin mazauna yankin, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan Muhalli a jihar, Architect Abdulmojeed Mogbonjubola ya ce gwamnantin ba ta da wani zabi illa hakan.

Abdulmojeed ya ce an dauki matakin ne saboda yawan matsalolin da ake samu tsakanin mazauna wurin da cocin.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun rufe mashigar shiga unguwar don hana mambobin cocin halartar bauta.

Wane gargadi gwamnatin ta yi?

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar ba za ta nade hannunta irin wannan lamari na faruwa ba karkashin ikonta.

Ya ce:

“Jami’an ma’aikatar sun samu korafe-korafe daga jama’a da ke kusa da cocin kan yawan damunsu da kara.
“Jami’an sun nadi yawan karar da ke fita a cocin tun daga fara bautar a rana wanda suka fahimci ya haura ka’idar yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya dakatar da kwamishina 1 da wasu manyan jiga-jigan gwamnati kan abu 1 tal

“Saboda haka, an bayyana cocin na fitar da kara da ya wuce ka’ida wanda ke damun jama’ar yankin.”

Har ila yau, kwamishinan ya gargadi ci gaba da damun jama’a da wuraren addinin ke yi da kuma wuraren shakatawa, cewar Daily Post.

Sauran wuraren da aka yi wa gargadin su sun hada da kamfanoni da kasuwanni inda ya ce duk wadanda suka saba dokar za su fuskanci hukunci.

Majalisar Oyo za ta kama shugaban Fulani

Kun ji cewa, Majalisar jihar Oyo ta bukaci kwamishinan ‘yan sanda da ya cafke shugaban Fulani a yankin Iwojowa a jihar.

Ana zargin Seriki Chumo da hannu a kisan wani manomi da kuma jami’in tsaron Amotekun a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.