Kotun Koli Ce Kadai Za Ta Tilasta Ni, Gwamnan PDP Ya Yi Fatali da Kotun Tarayya, Ya Fadi Dalili

Kotun Koli Ce Kadai Za Ta Tilasta Ni, Gwamnan PDP Ya Yi Fatali da Kotun Tarayya, Ya Fadi Dalili

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya sha alwashin ba zai biya tsaffin ciyamomi ko sisi ba a jihar
  • Gwamnan ya bayyana haka ne a birnin Ibadan da ke jihar a ranar Asabar 23 ga watan Disamba
  • Hakan ya faru ne bayan tsaffin ciyamomin sun maka gwamnan a kotu kan basuka biliyan hudu da suke bin gwamnatin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce ko sisi ba zai biya basukan ciyamomi ba har sai Kotun Koli ta umarce shi.

Makinde ya bayyana haka ne a birnin Ibadan da ke jihar a ranar Asabar 23 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Kano: Kotun ta tsare matashi kan zargin caka wa abokinsa wuka a ciki, wanda ake zargi ya magantu

Gwamnan PDP ya sha alwashin ba zai bi dokar kotu ba
Gwamna Seyi Makinde ya sha alwashin ba zai biya basukan ciyamomi ba. Hoto: Seyi Makinde.
Asali: Facebook

Mene ya jawo rikicin a Oyo?

Wannan ya faru ne bayan gwaman ya kore su daga kan kujerunshi bayan ya hau karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2019.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga bisani Kotun Tarayya ta rufe asusun bankunan jihar guda 10 kan basukan ciyamomin da suke bin gwamnati.

Da ya ke martani, Makinde ya ce ba zai taba biyansu ko sisi ba sai dai idan Kotun Koli ce ta umarce shi.

Ya ce ba zai bi uamrnin ba har sai ya tabbatar duk wani tsarin doka ya bi kuma ya kure matakin shari'a, cewar Daily Trust.

Wane martani gwamnan Oyo ya yi?

Ya kara da cewa korar ciyamomin a shekarar 2019 babu kuskure a ciki saboda ba a zabe su yadda doka ta tanadar ba.

Makinde ya bayyana cewa hukuncin babbar kotun Tarayya da ke Abuja ya sabawa dokar kasa da tsarin kotuna, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Tsaka mai wuya: Saurayi ya kashe budurwarsa bayan ta nemi ya biya ta kudin gamsar da shi

Ya ce:

"Dukkan tsaffin ciyamomin ba za su samu ko sisi ba har sai Kotun Koli ta umarce mu da mu biya.
"Ba zan taba biyan wadanda basu kamata ba, wannan gwamnati ce da take bin dokar kasa."

Kotu ta rufe asusun bankunan Oyo

A wani labarin, Babbar Kotun Tarayya ta rufe asusun bankunan jihar Oyo guda 10 kan basukan tsaffin ciyamomi.

Kotun ta dauki matakin ne bayan gwamnan ya kori dukkan ciyamomin kananan hukumomi a shekarar 2019 wadanda 'yan APC ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel