Tsadar Rayuwa: Gwamnan PDP Ya Tausayawa Ma’aikata, Ya Tsawaita Biyan Kudin Rage Radadi Har Wata 6

Tsadar Rayuwa: Gwamnan PDP Ya Tausayawa Ma’aikata, Ya Tsawaita Biyan Kudin Rage Radadi Har Wata 6

  • Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya yi alkawarin tsawaita biyan kudaden rage radadin cire tallafi har watanni shida
  • Gwamnan ya amince da hakan ne yayin da ake cikin wani hali ganin yadda tsadar rayuwa ya yi katutu a kasar baki daya
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wasu ma'aikatan jihar Gombe kan wannan mataki da Gwamna Makinde ya dauka a jiharsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Oyo – Yayin da ake cikin mawuyacin halin tsadar rayuwa, Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya saka ma’aikata hawaye a jihar.

Makinde ya amince da tsawaita biyan kudin rage radadi har na tsawon watanni shida bayan wa’adin ya kare, cewar Channel TV.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tsohon shugaban kasa ya yi magana, ya bayyana abin da ya ke tsoron zai faru

Gwamnan PDP ya gwangwaje ma'aikatan jiharsa yayin da ake cikin wani hali
Gwamna Makinde na jihar Oyo Ya Tsawaita Biyan Kudin Rage Radadi Har Watanni 6. Hoto: Seyi Makinde.
Asali: Facebook

Nawa Makinde ya amince zai biya ma'aikata?

Idan ba a manta ba, Makinde a ranar 6 ga watan Octobar 2023 ya amince da biyan naira dubu 15 ga ma’aikatan don rage musu radadin cire tallafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, ya kuma tsawaita biyan kudaden ga ‘yan fansho a jihar wanda ya ke biyansu naira dubu 25 a jihar.

Tun farko daman wa’adin biyan kudaden na watanni shida zai kare ne a watan Maris na wannan shekara da muke ciki.

Martanin gwamnan kan jita-jita

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin kaddamar da wasu tagwayen hanyoyi a yau Juma’a 16 ga watan Faburairu, kamar yadda The Nation ta tattaro.

Har ila yau, gwamnan ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa gwamnonin jam’iyyar PDP ba sa biyan albashin ma’aikata.

Wannan na zuwa ne yayin da al'ummar kasar suke cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa da kuma tashin farashin kaya.

Kara karanta wannan

Yadda wani mutum ya hallaka makwabcinsa saboda akuya, ya shiga hannun ‘yan sanda

Legit Hausa ta ji ta bakin wasu ma'aikatan jihar Gombe kan wannan mataki na Gwamna Makinde:

Inuwa Muhammad Ahmed da ke ma'aikatar ilimi ya roki Gwamna Inuwa da ya yi koyi da Makinde wurin rage wa mutane radadin da ake ciki.

Zaradden Muhammad da ke Hukumar Daukar Malamai a jihar ya ce:

"Tabbas abin da gwamnan ya yi ya nuna tausayawa ga al'ummarsa, muna kira da gwamnanmu da ya yi koyi da irin wannan mataki.

Wani da ya bukaci sakaye sunansa ya ce daman Gwamna Inuwa ba mutum ne mai son irin haka ba, dubu 10 da ya ke bayarwa ma don ta zama dole ce.

Buni zai biya ma'aikata dubu 35

Kun ji cewa, Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya amince da biyan naira dubu 35 ga ma’aikatan jihar.

Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin mawuyacin hali bayan cire tallafin man fetur a kasar a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel