Tinubu, Shettima da Gwamnoni Sun Dira Ibadan Don Taya Akande Murnar Cika Shekera 85

Tinubu, Shettima da Gwamnoni Sun Dira Ibadan Don Taya Akande Murnar Cika Shekera 85

  • Garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo ya yi cikar kwari yayin da tsohon shugaban APC na kasa, Bisi Akande ya cika shekaru 85
  • Tuni manyan masu ruwa da tsaki a Najeriya suka fara hallara a cibiyar taro na kasa da kasa da ke jami'ar Ibadan don taya shi murna
  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wanda aka wakilta, mataimakin Shugaban kasa, Kashim Shettima da wasu gwamnoni duk sun hallara

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ibadan, jihar Oyo - Manyan jiga-jigan Najeriya sun fara isa cibiyar taro na kasa da kasa da ke jami'ar Ibadan, domin taya tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif Bisi Akande, murnar cika shekaru 85 a duniya.

Kara karanta wannan

Betta: Gbajabiamila ya amince da N2bn ba tare da izinin Tinubu ba? Fadar shugaban kasa ta yi martani

Yayin taron an kuma tsara za a kaddamar da wata gidauniya ta Adebisi Akande, rahoton The Nation.

Haka kuma za a yi gudanar da wata makabala kan shugabanci karkashin jagorancin gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.

Bisi Akande ya cika shekaru 85 a duniya
Tinubu, Shettima da gwamnoni sun dira Ibadan don taya Akande murnar cika shekera 85 Hoto:MHR Clement Akanni
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin manyan bakin da suka fara halartar wajen sun haɗa da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo Olu ya wakilta.

Sauran sun haɗa da mataimakin shugaban kasa Kashim Shattima, da gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum.

An tsara taron rukuni-rukuni, inda aka zabi shugaban kasa da mataimakinsa su tsaya a matsayin manya baki a wajen, kuma Kashim Shattima na daga cikin masu gabatar da jawabi.

Su wanene suka halarci taron?

Sauran gwamnonin da suka halarci wajen sun haɗa da na Ogun Dapo Abiodun, na Ekiti Abiodun Oyebanji, da na Osun Ademola Adeleke.

Kara karanta wannan

Bwala: Hadimin Atiku ya faɗi abu 1 da zai yi idan Shugaba Tinubu ya naɗa shi muƙami a gwamnati

Akwai ministocin Tinubu da suma sun hallara a wajen da suka haɗa da ministan makamashi, Cif Adebayo Adelabu da takwaransana tattalin arziki Adegboyega Oyetola da sauran manyan baki, rahoton Vanguard.

Tinubu ya hadu da Obasanjo a Imo

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta kawo a baya cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo sun hadu a wajen rantsar da Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo.

An dai rantsar da Uzodimma ne a matsayin gwamnan jihar Imo a karo na biyu a garin Owerri, babban birnin jihar Imo a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu.

Wannan ita ce karo na farko da shugabannin biyu ke haduwa tun bayan babban zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel