“Ruwan Sama a Janairu”: Mutane Sunyi Martani Yayin Da Ruwan Sama Na Farko Ya Sauka a Ibadan a 2024

“Ruwan Sama a Janairu”: Mutane Sunyi Martani Yayin Da Ruwan Sama Na Farko Ya Sauka a Ibadan a 2024

  • An samu saukar ruwan sama na farko a garin Ibadan a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairun 2024
  • Mazauna Ibadan, babban birnin jihar Oyo sun nuna matukar farin ciki ga wannan ni'ima da ta saukar masu
  • Sun ce wannan wata alama ce da ke nuna an shiga sabuwar shekara a sa'a, kuma cewa ruwan sama zai sauka da wuri a bana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ibadan, jihar Oyo - Mazauna garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, sun ga saukar ruwan sama na farko a shekarar 2024 a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairu.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya fara ne da misalin karfe 3:40 na safe kuma ya ci gaba har tsawon kimanin mintuna 40, inda aka kammala da misalin karfe 4:20 na safe.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Mutum uku da aka sace sun mutu a kokarin gudowa daga hannun yan bindiga

An samu ruwan sama na farko a Ibadan
“Ruwan Sama a Janairu”: Mutane Sun Yi Martani Yayin da Ruwan Sama Na Farko Ya Sauka a Ibadan a 2024 Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Wannan ruwan sama da da ya sauka ba zato babu tsammani, ba tare da walkisa, iska mai karfi da tsawa ba ya zuba a yankunan Omi-Adio, karamar hukumar Ido, karamar hukumar Ibadan ta Kudu maso Yamma, da sauran sassa daban-daban na birnin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mazauna sun yi martani ga ruwan sama mai ban mamaki

Mazauna yankin sun yi maraba da saukar ruwan saman cike da farin ciki, suna masu daukar sa a matsayin "albarkar sabuwarar shekara."

Mista Paul Ademola, wani mazaunin yankin Omi Adio, ya nuna jin dadinsa kan saukin da aka samu daga zafin da ake zabgawa da yamma da kuma sanyin safiya da aka samu sakamakon ruwan sama mai sanyaya rai.

Ya ce:

“Haka zalika an samu sauki daga kura na lokacin dari wanda lalacewar hanya ke kara ta'azzara lamarin, wanda ke haifar da cututtuka a tsakanin mazauna Omi-Adio.

Kara karanta wannan

Kaico: 'Yan sanda sun kama magidanci kan ‘dabawa’ matarsa wuka a Yobe

"Ina ganin yana da kyau karamar hukumar ta ba da kulawar gaggawa wajen gina hanyoyin."

Mista Nicholas Olabanji, wani manomi, ya bayyana cewa ruwan sama abin farin ciki ne, kuma alama ce ta samun ruwan sama da wuri a wannan shekara.

Wata da ke siyar da abubuwa a bakin hanya, Misis Romoke Alao, ta bayyana irin wannan ra’ayi, inda ta yi la’akari da cewa ruwan sama albarka ne kuma kyakkyawar alama a shekarar nan.

An rahoto cewa wasu yankuna a garin Ibadan kamar su Oke-Itunu da Mokola a Ibadan ta Kudu maso Yamma basu samu ruwan sama ba, rahoton Peoples Gazzatte.

Walkiya ta hallaka dalibai

A wani labarin kuma, mun ji cewa walkiya ta kashe dalibai uku na makarantar babbar sakandare (SS3) a karamar hukumar Awka ta Kudu a jihar Anambra a ranar Asabar, Daily Trust ta ruwaito.

Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Najeriya (NAN) cewa, walkiyar ta rufta da dalibai maza tara ne da ke buga wasan kwallon kafa da takwarorinsu a filin makarantar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel