Abun Bakin Ciki Ya Sake Faruwa a Ibadan Yayin da Gobara Ta Tashi a Ofishin INEC, An Yi Karin Bayani

Abun Bakin Ciki Ya Sake Faruwa a Ibadan Yayin da Gobara Ta Tashi a Ofishin INEC, An Yi Karin Bayani

  • Ofishin hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) a karamar hukumar Ibadan ta Kudu maso Gabas ta kama da gobara
  • Kwamishinan hukumar zabe na jihar, Dr Adeniran Tella, ya tabbatar da tashin gobarar a cikin wata sanarwa
  • An tattaro cewa al'amarin ya afku ne da misalin karfe 10:30 na safiyar Juma'a, 26 ga watan Janairu, kasa da makonni biyu bayan faruwar wani mummunan al'amari a jihar

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Ibadan, jihar Oyo - Hukumar zabe a jihar Oyo ta tabbatar da tashin gobara a ofishinta da ke karamar hukumar Ibadan ta Kudu maso Gabas.

Wata sanarwa da Dr Adeniran Tella, kwamishinan zabe na jihar ya saki a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ta bayyana cewa gobarar ta faru ne da misalin karfe 10:30 na safiyar Juma'a, 26 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

A karshe, rundunar sojin saman Najeriya ta nemi afuwar mutane kan kuskuren kashe bayin Allah a arewa

Ofishin INEC ya kama da wuta a Oyo
Abun Bakin Ciki Ya Sake Faruwa a Ibadan Yayin da Gobara Ta Tashi a Ofishin INEC, An Yi Karin Bayani Hoto: Seyi Makinde
Asali: Facebook

Yayin da har yanzu ba a tantance ainihin musabbabin tashin gobarar ba, ana hasashen cewa ta samo asali ne daga karfin wutar lantarki, kamar yadda kwamishinan zaben ya bayyana, rahoton PM News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tabbatar da cewar ba a rasa rai ba sannan ya fayyace cewa kayan aiki kawai aka rasa.

Tella ya kara jaddada cewa lamarin ba zai yi tasiri a zaben mazabar Saki ta Yamma da za a yi a ranar 3 ga watan Fabrairu mai zuwa ba, rahoton Naija News.

Garin Ibadan ya yi fama da abubuwan bakin ciki da dama cikin kasa da makonni biyu, wanda na baya-bayan nan da ya afku shine tashin abun fashewa a yankin Bodija da ke garin wanda ya kai ga rasa rayuka da dukiyoyi.

Gobara ta lakume gidaje 50 a Benue

Kara karanta wannan

An kara kashe bayin Allah a jihar arewa duk da sa dokar kulle, Atiku ya maida martani mai zafi

A wani labarin, mun ji cewa wata tsohuwa ƴar shekara 80 ta ƙone ƙurmus a wata gobara da ta ƙone gidaje 50 a ƙauyen Tse-Agubor Gyaruwa da ke gundumar Tsambee-Mbesev a ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma a jihar Benue.

Shugaban ƙauyen da abin ya shafa, Cif Ayatse Agubor, ya shaida wa manema labarai a Makurdi cewa, gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Lahadi, yayin da mutanen ƙauyen ke aiki a gonakinsu, cewar rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel