Nijar: Ministan Tsaron UK Ya Gana da Hafsoshin Tsaro a Abuja, Ya Goyi Bayan ECOWAS

Nijar: Ministan Tsaron UK Ya Gana da Hafsoshin Tsaro a Abuja, Ya Goyi Bayan ECOWAS

  • Ministan Burtaniya ya gana da ministocin tsaro da hafsoshin tsaron Najeriya a birnin Abuja ranar Laraba
  • James Heappey MP ya jaddada goyon bayan ƙasar Burtaniya ga yunkurin ECOWAS na dawo da mulkin Dimokuraɗiyya a Nijar cikin lumana
  • Taron ya kuma tattauna kan batun inganta alaƙa tsakanin kasashen biyu a bangaren abinda ya shafi tsaro

FCT Abuja - Ministan kula da rundunar sojin Burtaniya, James Heappey MP, ya gana da manyan ƙusoshin ma'aikatar tsaro da hafsoshin tsaron Najeriya a Abuja.

Wannan taro ya maida hankali ne kan yauƙaƙa dangatakar tsaro da ke tsakanun ƙasashen biyu da kuma tattauna batun juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar.

Ministan UK tare da manyan ƙusoshin tsaron Najeriya.
Nijar: Ministan Tsaron UK Ya Gana da Hafsoshin Tsaro a Abuja, Ya Goyi Bayan ECOWAS Hoto: @channelstv
Asali: Twitter

Channels tv ta ce yayin wannan ziyara, Ministan tsaron UK ya haɗu da manyan kuoshin ma'aikatar tsaro da hafsoshin tsaro 2 a Abuja ranar Laraba, 23 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

"Akwai Babbar Matsala" Fitaccen Malami Ya Bayyana Hukuncin da Kotu Zata Yanke Kan Nasarar Tinubu a 2023

Manyan jiga-jigan gwamnati da ministan ya gana da su

Mista Heappey ya samu ganawa da ministan tsaro, Muhammad Badaru, ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, babban hafsan tsaron ƙasar nan, Christopher Musa da hafsan sojin ƙasa, Taoreed Lagbaja.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Haka zalika ya zauna da shugaban hukumar ƙungiyar bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS), Omar Touray, kamar yadda Tribune ta rahoto.

UK na goyon bayan ƙungiyar ECOWAS

A jawabinsa, Mista Heappey ya jaddada cewa ƙasar Burtaniya (UK) na goyon bayan ƙungiyar ECOWAS a kokarinta na bin hanyar maslaha wajen tabbatar da mulkin Dimokuraɗiyya ya dawo a Nijar.

A kalamansa, Ministan UK ya ce:

"Na yi farin cikin dawowa Najeriya karo na uku cikin shekaru uku.
“Rundunar sojin Burtaniya da na Najeriya na da daɗadɗen hadin gwiwa ta yadda za mu ci gaba da magance ta’addanci da sauran matsalolin tsaro a yammacin Afirka da gaɓar tekun Guinea."

Kara karanta wannan

"Akwai Haske": Abdulsalami Ya Yi Magana Kan Tattaunawarsu Da Sojojin Juyin Mulkin Nijar

"Burtaniya tana goyon bayan ECOWAS wajen yin kira da a maido da tsarin mulkin dimokuradiyya cikin lumana a Nijar kuma za mu yi aiki tare da sauran abokanmu a yammacin Afirka don tallafa musu a kan wannan manufar."

Ya ce Burtaniya ta fahimci kokarin diflomasiyya da Najeriya ke yi na maido da dimokuradiyya a Nijar cikin lumana, ta hanyar kasancewarta mamba a kungiyar ECOWAS.

Ministocin da Shugaba Tinubu Ya Nada Sun Yi Kadan a Najeriya Inji Jigon APC

A wani labarin na daban Mamban kwamitin APC na miƙa mulkin shugaban kasa ya ce ministocin da shugaba Bola Tinubu ya naɗa sun yi kaɗan a Najeriya.

Wannan kalamai na Mista Audu na zuwa ne yayin da ke cece kuce da sukar da ake yi kan cewa shugaba Tinubu ya naɗa ministoci har guda 45.

Asali: Legit.ng

Online view pixel