Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Sanar da Garkame Wasu Kasuwannin Shanu 8 Yankunan Jihar

Gwamnatin Jihar Zamfara Ta Sanar da Garkame Wasu Kasuwannin Shanu 8 Yankunan Jihar

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana garkame kasuwannin shanun jihar biyo bayan barkewar rashin tsaro a wasu sassan jihar
  • An bayyana cewa, an samu sake bullar satar shanu a jihar da ke yawan fuskantar sace-sace da garkuwa da mutane a Arewa
  • Gwamnatin jihar ta daura alhakin tabbatar da an bi dokar da gwamnatin ta sanya a wannan karon, musannan wasu kasuwanni takwas

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da rufe kasuwannin shanu 8 nan take a kananan hukumomi biyar na jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da al’adu na gwamnatin, Mannir Haidara ya fitar ranar Lahadi a Gusau, Punch ta ruwaito.

Ya ce majalisar tsaron jihar ta amince da rufe kasuwannin shanun na wucin gadi ne yayin taron da ta gudanar a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Kitimurmura yayin da gwamnatin jiha ta garkame fitaccen gidan rediyo da TV

An garkame kasuwannin shanu a Zamfara
Zamfara: Yadda aka garkame kasuwar shanu | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wasu kasuwanni abin ya shafa?

A cewarsa, matakin na daga cikin matakan dakile sabbin hare-hare da satar shanu da ake fuskanta a sassan jihar, rahoton Ripples Nigeria.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar sanarwar:

“An dauki matakin ne biyo bayan sake bullar satar shanu da ake yi a yankunan da lamarin ya shafa.
“Kasuwannin shanun da abin ya shafa su ne; Danjibga da Kunchin-Kalgo a kasuwannin shanun Tsafe, Bagega da Wuya a cikin garin Anka.
“Sauran su ne Dangulbi da Dansadau a Maru, Dauran a Zurmi da Nasarawar Burkullu a karamar hukumar Bukkuyim.”

Su wa za su tabbatar da an bi dokar?

Haidar ya ce majalisar ta dorawa hukumomin tsaro da hukumar kula da lafiyar dabbobi da kiwo alhakin tabbatar da bin doka da oda, Solace Base ta tattaro.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara Ta Sanar Da Rufe Kasuwanni a Ƙananan Hukumomi 5 Na Jihar, Ta Ba Da Dalili

Ya nanata kudurin gwamnatin Gwamna Dauda Lawal na maido da zaman lafiya a jihar da ke yawan fuskantar barnar ‘yan bindiga.

Ana samun karancin shanu a wasu jihohin?

An samu karancin shigowar abubuwa da suka hada da shanu, rakuma, tumaki, dabino da sauransu daga jamhuriyar Nijar biyo bayan kulle iyakokin da aka yi.

Hakan ya biyo bayan hambarar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum da sojojin jamhuriyar Nijar din suka yi a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.

An yi ittifakin cewa kaso mafi yawa na dabbobin da ake yankawa a sassa daban-daban na Najeriya suna zuwa ne daga jamhuriyar Nijar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel