Tsohon Jigon APC Ya Fallasa Ainihin Abin da Ya Jawo Tinubu Yake Yunwar Yaki da Nijar

Tsohon Jigon APC Ya Fallasa Ainihin Abin da Ya Jawo Tinubu Yake Yunwar Yaki da Nijar

  • Dr. Usman Bugaje ya gabatar da takarda da ya nuna kuskuren ECOWAS na shiga yaki da kasar Nijar
  • Tsohon ‘dan majalisar bai goyon bayan a aukawa mutanen da ke da kyakkyawar alaka da Najeriya
  • Masana sun soki garajen da kungiyar ECOWAS ta yi na barazanar dawo da Mohammed Bazoum

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kaduna - A wata lacca ta musamman da aka gudanar a cibiyar ITN a garin Zariya, jihar Kaduna, an tattauna game da sabon yunkurin kungiyar ECOWAS.

Tsohon ‘dan majalisar wakilan tarayya, Dr. Usman Bugaje ya na cikin wadanda su ka gudanar da takarda kan barazanar da ECOWAS ta ke yi wa kasar Nijar.

Usman Bugaje ya dauko alakar Najeriya da makwabciyarta da yadda Nijar ta ke taimakawa kasar nan a yakar ta’addancin ‘yan bindiga da Boko Haram.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Zaftare Yawan Jami'an Gwamnati Masu Fita Kasar Waje Saboda Rage Kashe Kudi

TINUBU
Bola Tinubu da Shugabannin ECOWAS Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Masanin ya ce tun farko gwamnatin tarayya da shugabannin ECOWAS sun yi kuskure wajen gaggawar barazanar dawo da mulkin farar hula a Nijar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meya jawo Tinubu ya ke son ayi yaki?

‘Dan siyasar ya ce a hasashensa, watakila abin da ya faru da jirgin NADECO a Nijar a lokacin Janar Sani Abacha ya yi tasiri wajen matakin da aka dauka.

Bola Tinubu ya na cikin jagororin kungiyar NADECO wanda hukumomin jamhuriyyar ta Nijar su ka damka mutanensu ga Najeriya a lokacin mulkin sojin.

Bayan haka, ‘dan siyasar ya ce idan har yaki ya barke da makwabtan, shugaban Najeriya zai iya samun iko na musamman da zai cigaba da yin mulki.

Idan ana bibiye da mu, hakan ya na zuwa ne a lokacin da shari’ar zaben shugaban kasa tsakanin Bola Tinubu da Atiku Abubakar da Peter Obi ya yi zabe.

Kara karanta wannan

Rikicin Jamhuriyar Nijar: Jerin Manyan Abubuwa 5 Da Suka Faru Cikin Makon Nan

Baya ga haka, Dr. Bugaje ya ce an taso shugaba Tinubu a gaba a kan zargin badakalar takardun shaidar karatu, hakan ya jawo ya ke neman karbuwa a waje.

A laccar, tsohon mai ba mataimakin shugaban Najeriya shawara ya ce ba za su taba yarda a yaki Nijarawa ba wanda su ke iyaka da Arewacin kasar nan.

Ra'ayin Dr. Sadique Mohammed

Shi ma a jawabinsa, Dr. Sadique Mohammed ya ce kafin bada wa’adin dawo da farar hula, ya kamata shugaban kasa ya tuntubi ma’aikatar harkokin waje.

Babban masanin ya ce idan wa’adi irin wanda ECOWAS ta bada ya wuce ba tare da an yi rawar gani ba, hakan zai jawo a ji kunya, kuma a fadi babu nuayi.

Laccar ta nuna zai yi wahala Najeriya ta iya yakar Nijar saboda fadin kasar ta, sannan yakin zai iya jawo rikici ya barke tsakanin kasashen Afrika.

Tinubu bai son 'Yan Arewa - Naja'

Kara karanta wannan

Za a yi ta: Faransa ta daga yatsa ga sojin Nijar bayan umarnin korar jakadanta a kasar

An ji labari Naja’atu Muhammad ta na da ja game da yakar Nijar, ta na ganin an saba ka’idojin damukaradiyyar da ECOWAS ta ke so a dawwamar.

Tun can Naja’atu Muhammad ba ta yarda da kamun ludayin Bola Ahmed Tinubu, har gobe ta na ganin shugaban bai nufin yankin Arewa da alheri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel