Badaru da Matawalle Sun Yi Alkawarin Kawo Sauyi a Tsaro Cikin Shekara Daya

Badaru da Matawalle Sun Yi Alkawarin Kawo Sauyi a Tsaro Cikin Shekara Daya

  • Ministocin tsaro, Muhamnad Badaru da Bello Matawalle sun yi alkawarin kawo sauyi a yanayin tsaron Najeriya cikin shekara ɗaya
  • Tsoffin gwamnonin sun shiga ofis a rana ta farko yau Talata awanni 24 bayan rantsuwar kama aiki
  • Sun ce zasu yi duk mai yiwawa ba tare da gajiya wa ba wajen cika burin shugaban ƙasa da 'yan Najeriya kan tsaro

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Ministan tsaro, Muhammad Badaru Abubakar da ƙaramin ministan tsaro, Muhammad Bello Matawalle, sun yi wa yan Najeriya alƙawari mai girma.

Sabbin ministocin biyu sun yi alkawalin kawo sauyi "na ban mamaki" a fasali da tsarin tsaron Najeriya a cikin shekara guda.

Ministocin tsaro, Badaru Abubakar da Bello Matawalle.
Badaru da Matawalle Sun Yi Alkawarin Kawo Sauyi a Tsaro Cikin Shekara Daya Hoto: Journalist KC
Asali: Facebook

Badaru da Matawalle sun ɗauki wannan alkawari ne yayin da suke jawabi ga 'yan jarida ranar Talata a ɗan kwarya-kwaryan bikin kama aiki da aka shirya musu a ma'aikatar tsaro da ke Abuja.

Kara karanta wannan

“Ina Dalili”: Suka, Martani Kan Nadin Hadimai Mata 131 Da Gwamnan Arewa Ya Yi

Channels tv ta tattaro cewa wannan na zuwa ne awanni 24 bayan Ministocin sun yi rantsuwar kama aiki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ba zamu ci amanar shugaba Tinubu ba - Badaru

Badaru, tsohon gwamnan Jigawa da ya gabata, ya tabbatar wa yan Najeriya cewa saboda kasar nan, shi da karamin minista ba za su iya cin amanar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ba su ba.

A cewarsa, a cikin shekara ɗaya tal, za a samu sauye-sauye na ban mamaki domin inganta harkokin tsaro a kasar nan, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Ya kuma yi alkawarin cewa shi da Matawalle za su yi iya bakin kokarinsu wajen ganin sun fidda Tinubu kunya, wanda shi da ɗaukacin ‘yan Nijeriya ke da burin ganin an tabbatar da tsaro a lungu da saƙo na Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Zai Tsamo Mutane Miliyan 136 Daga Talauci Kuma Zai Samar da Ayyukan Yi 10m, Bayanai Sun Fito

A nasa bangaren, Matawalle ya ba da tabbacin cewa ma’aikatar ba za ta yi kasa a gwuiwa ba wajen kafa matakan tsaro masu karfi da za su iya tunkarar duk wata barazana.

Kafin wannan muƙami da shugaba Tinubu ya naɗa shi, Matawalle ya riƙe kujerar gwamnan Zamfara, jihar da ake hasashen matsalar tsaro ta yi wa ƙatutu a Arewa maso Yamma.

Abinda 'Yan Bindiga Suke Buƙata a Jihar Zamfara

A wani rahoton kun ji cewa Babbar buƙatar da yan bindiga su ke nema daga wurin gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana.

Ɗan majalisar tarayya, Kabiru Ahmadu, ya ce yan bindigan jeji na son a tattauna da su shiyasa suka ƙara zafafa kai hare-hare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel