Abinda 'Yan Bindiga Suke Buƙata a Jihar Zamfara, Dan Majalisa Ya Tona Gaskiya

Abinda 'Yan Bindiga Suke Buƙata a Jihar Zamfara, Dan Majalisa Ya Tona Gaskiya

  • Babbar buƙatar da yan bindiga su ke nema daga wurin gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana
  • Ɗan majalisar tarayya, Kabiru Ahmadu, ya ce yan bindigan jeji na son a tattauna da su shiyasa suka ƙara zafafa kai hare-hare
  • A cewarsa tsohon gwamna Bello Matawalle ya musu duk abinda su ke buƙata amma daga baya suka ci gaba da aikata ta'addanci

Zamfara - Ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Gusau/Tsafe, Kabiru Ahmadu, ya bayyana babban abinda 'yan bindiga ke buƙata daga gwamnati.

Ya ce 'yan bindigan daji sun ƙara matsa ƙaimi wajen kai hare-hare kan mutane a jihar Zamfara saboda su tilasta wa gwamnati tattauna da su domin neman maslaha.

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal.
Abinda 'Yan Bindiga Suke Buƙata a Jihar Zamfara, Dan Majalisa Ya Tona Gaskiya Hoto: Dauda Lawal
Asali: UGC

Honorabul Ahmadu ya bayyana haka ne a wata hira da Channels tv cikin shirinsu na Sunrise Daily.

Kara karanta wannan

"Abuja Ba Fatakwal Ba Ce": Hadimin Atiku Ya Gargadi Wike, Ya Gaya Masa Abin Da Yakamata Ya Yi

A cewarsa, 'yan bindiga suna son gwaamnati ta musu afuwa amma a ganinsa hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya tunatar da cewa tsohuwar gwamnatin jihar ta jaraba tattaunawar neman sulhu da 'yan bindiga amma hakan bai kawo ƙarshen matsalar ba.

Haka zalika Ahmadu ya ƙara da cewa ‘yan bindigar na amfani da lokacin damina wajen kai hare-hare, domin sojoji ba za su iya shiga wasu yankunan ba saboda rashin kyawun hanya.

Abinda 'yan bindiga suke bukata daga gwamnati a Zamfara

A rahoton Daily Trust, Ɗan majalisar ya ce:

"Dalilin da ya sa ake yawan kai hare-hare a koda yaushe shi ne, 'yan fashin suna son mu amsa bukatarsu, suna son mu tattauna da su. Muna ganin hakan ba ita ce mafita ba domin gwamnati baya ta yi amma bai amfani ba."

Kara karanta wannan

“Ina Dalili”: Suka, Martani Kan Nadin Hadimai Mata 131 Da Gwamnan Arewa Ya Yi

“Suna kokarin tsorata mutane ta hanyar kai hare-hare a ko da yaushe kuma suna cin gajiyar damina ganin cewa akwai wasu wuraren da sojoji ba sa iya shiga saboda babu hanya."
"Bukatarsu kawai mu tattauna da su kuma mu yi musu afuwa wanda duk mun amince cewa hakan ba zai yuwu ba."

Ɗan majalisar ya ƙara da cewa Abdul'aziz Yari ya jaraba tattauna wa da su amma basu daina ba, Matawalle ya tattauna dasu, ya jawo su a jiki amma daga baya suka ci gaba da kai hari.

Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Gonan Sanata

A wani rahoton kuma Wasu yan bindiga da ake kyautata zato masu garkuwa da mutane ne sun kai hari gidan gonar tsohon Sanatan Kwara ta kudu.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun halaka Manajan da ke kula da gidan gonan kuma ɗan uwan tsohon Sanatan yayin harin na ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Miyagun Yan Bindiga Sun Tattara 'Yan Bautar Ƙasa NYSC, Sun Yi Awon Gaba da Su a Arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel