Yan Bindiga Sun Fara Amfani Da Dabarun 'Yan Ta'adda Don Yin Barna, Sojoji

Yan Bindiga Sun Fara Amfani Da Dabarun 'Yan Ta'adda Don Yin Barna, Sojoji

  • Rundunar soji ta bayyana wasu dabaru da 'yan bindiga suka fara ɓullo wa da su a arewacin Najeriya
  • Babban hafsan rundunar sojin ƙasa, Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, ya ce sojoji ba zasu yi ƙasa a guiwa ba wajen murkushe yan ta'adda
  • Ya roki goyon bayan majalisar ɗinkin duniya domin dawo da zaman lafiya a sassan ƙasar nan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa 'yan bindiga da sauran masu aikata muggan laifuka sun fara ɗaukar dabarun 'yan ta'adda wajen aikata ta'addanci.

Rundunar ta ce 'yan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabashin Najeriya sun ɓullo da dabarun 'yan ta'adda wajen kai hare-hare kan al'umma.

Dakarun sojin Najeriya.
Yan Bindiga Sun Fara Amfanu Da Dabarun 'Yan Ta'adda Don Yin Barna, Sojoji Hoto: Nigerian Army
Asali: UGC

Ta ƙara da cewa kwararan shaidu sun bayyana a fili cewa sun fara amfani da abubuwan fashewa (IEDs) wajen aikata ta'addanci kan yan ƙasa masu bin doka, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan Juyin Mulkin Gabon, Shugaba Tinubu Ya Faɗi Ainihin Abinda Yake Jin Tsoron Ya Faru

Hafsan rundunar sojin ƙasan Najeriya, Janar Taoreed Abiodun Lagbaja, ne ya bayyana haka a hedkwatar hukumar soji da ke birnin tarayya Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya fallasa waɗannan dabarun da 'yan bindiga suka ɓullo da su ne yayin da ya karɓi baƙuncin mataimakin sakataren sashin yaƙi da ta'addanci na majalisar ɗinkin duniya, Vladimir Voronkov, ranar Alhamis.

Wane mataki rundunar take ɗauka?

Amma duk da haka, Hafsan rundunar sojin ya jaddada cewa duk dabarar ba zasu ɓullo da ita, sojoji da zasu yi ƙasa a guiwa ba wajen murƙushesu ta kowane hali.

Hafsan sojojin, ya ce rundunar a shirye take ta hada kai da kungiyar domin dawo da zaman lafiya a sassan kasar nan da ke fama da rikici, Vanguard ta tattaro.

Babban hafsan sojan ya nemi goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya da sauran sassanta kan shirin sauya tunanin ‘yan ta’addan da suka tuba.

Kara karanta wannan

An Bayyana Babban Abu 1 Da Ya Jawo Ƙaruwar Juyin Mulkin Sojoji a Nahiyar Afirka

Vladimir Voronkov ya yi alkawarin cewa majalisar za ta taimaki Najeriya wajen ganowa, bincike da kuma hukunta masu aikata laifukan da suka shafi ta'addanci.

Tsoron Juyin Mulki Ya Sanya Kungiyar AU Dakatar Da Kasar Gabon Daga Cikin Mambobinta

A wani rahoton kuma Kungiyar Tarayyar Afrika (AU), ta dakatar da ƙasar Gabon daga cikin mambobinta.

Kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar ne ya sanar da hakan a yayin wani taro na gaggawa da ya gadanar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel