Edo: Ana Fargabar Soja Ya Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki Motar Sojoji

Edo: Ana Fargabar Soja Ya Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki Motar Sojoji

  • Wasu 'yan bindiga sun yi wa motar sojojin Najeriya kwantan ɓauna, sun halaka soja ɗaya a babban birnin jihar Edo
  • Bayanai sun nuna sojoji huɗu ne a cikin motar sa'ilin da maharan suka farmake su ba zato ba tsammani ranar Laraba
  • Har yanzun hukumomin soji ko 'yan sanda ba su ce komai ba kan lamarin amma majiyoyi da dama sun tabbatar da harin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Benin City, Edo state - Wasu miyagun 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi wa motar dakarun sojin Najeriya kwantan ɓauna a Benin, babban birnin jihar Edo.

'Yan bindiga sun farmaki motar sintirin jami'an sojin ba zato ba tsammani, inda suka yi ajalin soja guda ɗaya a jihar Edo da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.

Jami'an hukumar sojin Najeriya.
Edo: Ana Fargabar Soja Ya Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Farmaki Motar Sojoji Hoto: channelstv
Asali: UGC

Rahoton Channels tv ya tattaro cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 2:00 na tsakar rana, a ranar Laraba da ta gabata a mahaɗar tituna ta farko da ke kan titin Akpakpava.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Hedkwatar 'Yan Sanda a Jihar PDP, An Rasa Rai

A cewar wasu majiyoyi daga yankin da lamarin ya faru, tsagerun 'yan bindigan sun yi wa motar sojojin kwantan ɓauna, wacce ke ɗauke da jami'an soji guda hudu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayanai sun nuna maharan sun buɗe wa sojojin da ke cikin motar wuta yayin da su ke kan hanyar zuwa yankin Ikpoba-Hill a cikin babban birnin jihar.

Har zuwa lokacin haɗa muku wannan rahoto, ana dakon tabbatar da faruwar lamarin a hukumance daga hukumomin da abin ya shafa.

Hukumar soji ta ɓinne jami'ai 20 a Neja

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar sojin Najeriya ke jimamin rasa sojoji 36 a jihar Neja da ke Arewa ta tsakiya a Najeriya.

Jami'an sojin sun rasa rayuwarsu ne a wani harin kwantan ɓauna da 'yan bindiga suka kai musu da kuma harbo jirgin rundunar sojin sama.

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa a ranar Jumu'a, rundunar soji ta gudanar da bikin ɓinne gawarwakin sojojinta 20 daga cikin waɗanda aka kashe a jihar Neja.

An Halaka Tsohuwar Shugabar Kotun Kostumare a Jihar Benuwai

Kun samu labarin cewa An shiga tashin hankali yayin da aka tsinci gawar wata shugabar Alkalai da ta yi ritaya a jihar Benuwai, Misis Margaret Igbeta.

Ana zargin cewa watakila an kashe marigayya mai shari'a ne kwana daya da ya gabata duba da yadda yanayin gawar ta ya nuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel