Dakarun 'Yan Sanda Sun Yi Artabu da Yan Bindiga a Jihar Katsina

Dakarun 'Yan Sanda Sun Yi Artabu da Yan Bindiga a Jihar Katsina

  • 'Yan sanda sun yi musayar wuta da 'yan bindiga a jihar Katsina, sun samu gagarumin nasara ranar Jumu'a
  • Kakakin yan sandan, ASP Aliyu Abubakar ya ce jami'ai sun samu nasarar ceto wani bawan Allah da aka sace a yankin Malumfashi
  • Kwamishinan 'yan sanda, Aliyu Musa, ya yaba wa dakarun 'yan sandan bisa jajircewar da suka nuna

Katsina state - Dakarun rundunar 'yan sanda reshen jihar Katsina sun yi artabu da 'yan bindiga da sanyin safiyar ranar Jumu'a, 25 ga watan Agusta, 2023 kuma sun samu nasara.

Punch ta tattaro cewa yayin musayar wuta da 'yan ta'addan, jami'an 'yan sanda sun kubutar da wani dattijo ɗan shekara 65, Hashim Yusuf, wanda aka sace a Hayin Gada, ƙaramar hukumar Malumfashi.

Kakakin yan sandan Katsina, ASP Aliyu Abubakar.
Dakarun 'Yan Sanda Sun Yi Artabu da Yan Bindiga a Jihar Katsina Hoto: punchng
Asali: UGC

Haka zalika dakarun rundunar 'yan sandan sun kuma yi nasarar ƙwato shanu 94, Tumaki 17 da kuma babura biyu daga hannun 'yan bindigan.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: An Kama Wanda Ake Zargi Da Hannu a Kashe Shugabar Alkalan Kotu a Arewacin Najeriya

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Katsina, ASP Abubakar Aliyu, shi ne ya tabbatar da wannan gagarumar nasara ranar Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi bayanin cewa jami'an tsaro sun samu labarin motsin 'yan bindigan da misalin karfe 2:30 na dare wayewar garin ranar Jumu'a, daga nan suka haɗa tawaga suka tarbe su.

Yadda yan sanda suka yi artabu da yan bindiga

Aliyu ya ƙara da cewa yayin da suka yi arangama ne aka yi musayar zuwa mai ban tsoro, wanda daga ƙarshe jami'ai suka ceci mutumin kuma suka kwato kayayyakin.

A kalamansa, kakakin 'yan sandan ya ce:

"A ranar 25 ga watan Agusta, caji ofis ɗin Kankara suka samu kiran gaggawa game da motsin wasu 'yan bindiga daga garin Hayin Gada a yankin Malumfashi, inda suka sace Hashim Yusuf, 65."
"Sun nufi hanyar ƙauyen Lafiya a yankin Kankara, Nan take yan sanda suka tunkari wurin inda suka ci karo da 'yan ta'adda ɗauke da AK47 da wasu muggan makamai suna ƙoƙarin gudumuwa da mutumin."

Kara karanta wannan

Gunin Sha'awa: 'Yar Sanda Mace Ta Samu Kyauta Mai Tsoka Kan Ƙin Karɓan Maƙudan Kuɗin Cin Hanci

"Yayin musayar wuta, dakarun 'yan sanda sun nuna jajircewa da gwarzantaka ba tare da gajiya ba har sai da suka tabbatar sun murƙushe barazanar kuma sun ceto mutumin."

Aliyu ya ce kwamishinan yan sandan Katsina, Aliyu Musa, ya yaba wa jami'an bisa namijin ƙoƙarin da suka yi a bakin aiki, jaridar Within Nigeria ta tattaro.

Duba da matakan da gwamnatin Katsina ke ɗauka domin tabbatar da tsaro, Legit.ng ta zanta da wasu mazauna jihar kuma a cewarsu hare-hare na ƙaruwa kwanan nan.

Wani malamin addinin Musulunci a yankin Ɗanja, Malam Yusuf, ya ce yana wa gwamna mai ci fatan alkairi amma akwai aiki babba a gabansa game da matsalar tsaro.

A kalamansa, Malamin ya ce:

"A zahirin gaskiya labaran da muka ji daga ƙananan hukumomin da matsalar ta fi yawa ba daɗi, a makon nan yan bindiga sun kai hare-hare mara daɗi. Ya zama dole gwamnati ta tashi tsaye."

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

"Gwamna ya zo Funtua kaddamar da rabon kayayyaki kwanan nan kuma ya faɗi matakan da yake ɗauka, kuma muna fatan za a samu nasara domin tsaro shi ne matakin farko na ci gaba."

Hukumar 'Yan Sanda Ta Musanta Ikirarin Ɗan Bindiga Ya Zama Gwamna a Neja

A wani labarin kuma Hukumar 'yan sanda ta ƙaryata rahoton da ke yawo cewa wani shugaban 'yan bindiga ya ayyana kansa a matsayin gwamnan Neja.

Kakakin 'yan sandan jihar, Wasi'u Abiodun, ya ce rahoton ƙanzon kurege ne kuma jami'an tsaro na aiki tukuru domin dawo da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262