Yaki da ta'addanci a Najeriya
Yunkurin kawo karshen ta'addanci da tsagerancin 'yan bindiga ya yi nisa. Gwamnatin Najeriya ta saye jiragen AH-1Z da kayan yaki daga hannun Amurka.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da sabuwar rundunar tsaro wacce za ta yi fito na fito da ƴan bindigan da suka daɗe suna addabar jihar.
Rahotanni sun nuna cewa an tsinto gawarwakin mutane 15 yanzu haka bayan wani hari da aka kai mai muni kan jama'a a yankin karamar hukumar Agatu, jihar Benue.
An sace ‘yan makarantar Apostolic Faith Group a Ekiti. Idan ana son ganin wadannan mutane, ‘yan bindigan sun bukaci a tanadi N100m a matsayin kudin fansa.
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya ƙaƙaba dokar zaman guda daga karfe 6 na safe zuwa 6 na yammacin kowace rana a garuruwa 2 masu faɗa da juna.
Wasu miyagu sun halaka shugabannin matasa biyu a jihar Delta ranar Litinin da ta gabata, Sanatan jihar ya yi Allah wadai da kisan gillan, ya nemi a ɗauki mataki.
Adadin wadanda aka yi garkuwa da su daga 2019 zuwa yau ya kai 17, 469 Rahoto ya nuna ana da labarin rayuka kusan 2, 500 da aka rasa a karkashin Bola Tinubu.
Tsagerun ƴan bindiga sun kai sabon harin kan jami'an tsaro a wurin wasu masu sana'ar POS a jihar Imo, sun kashe ƴan sanda biyu da fararen hula biyu a harin.
Zagazola Makama ya tabbatar da cewa wani abun fashewa da ƴan ta'addan Boko Haram suka dasa ya yi ajalin akalla manoma 7 tare da jikkata wasu a jihar Borno.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari