Gwamnan APC Ya Tono Tushen Matsalar Ƴan Bindiga a Arewa, Ya Jero Hanyoyin Magance Su

Gwamnan APC Ya Tono Tushen Matsalar Ƴan Bindiga a Arewa, Ya Jero Hanyoyin Magance Su

  • Malam Uba Sani ya bayyana hanyoyin da ya kamata a bi domin kawo karshen matsalar tsaro a Arewa maso Yamma
  • Gwamnan ya ce tun asuli talauci ne da rashin aikin yi suka kawo matsalar tsaro, don haka bai kamata a bi matakin soji kaɗai ba
  • A cewarsa, akwai bukatar samun shugabanci wanda zai samar da ayyukan yi da yaye talaucin da ya addabi al'umma

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Gwamna Malam Uba Sani na jihar Kaduna ya bayyana abubuwan da suka haddasa matsalar ƴan bindiga da garkuwa da mutane a Arewa Maso Yamnacin Najeriya.

Gwamna Sani ya ce talauci da zaman kashe wando ne suka rikiɗa suka haifar da ƴan bindiga a shiyyar, inda yace ya zama wajibi a kawar da su domin samun zaman lafiya.

Kara karanta wannan

"Jama'a na shan wahala" Gwamna Abba na Kano zai gana da Tinubu kan muhimmin abu 1 tal

Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna.
Hanyar da Za a Bu a Kawo Karshen Yan Bindiga a Arewa Masi Yamma, Gwamna Hoto: Uba Sani
Asali: Facebook

Malam Uba Sani ya nuna muhimmancin samun jagoranci na gari idan har ana son ganin bayan waɗannan matsaloli a Arewa ta Yamma, Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sani ya kuma yabawa yaƙin da sojoji ke ci gaba da yi da ƴan bindiga yayin da hedkwatar tsaro ta tallafa wajen kafa sansanin Operation guda biyu (FOBs) a muhimman wurare.

Hanyoyin da za abi wajen kawar da ƴan bindiga

Gwamnan ya kuma ambaci bin hanyar lumana wajen tunkarar matsalar, yana mai cewa shugabanci na gari zai taka rawa wajen magance matsi wanda ke kawo tada kayar baya.

A cewarsa, tsare-tsaren da suka hada da gyara harkar ilimi, tallafawa manoma, da samar da ayyukan yi, na da matukar muhimmanci wajen kawar da talauci da rashin tsaro a yankin.

Baya ga ɗaukar matakin sojoji, Mista Sani ya ayyana shirin kafa asusun tsaro, wanda zai ba da damar haɗa gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu don inganta ayyukan tsaro.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya yi magana mai zafi bayan fashewar wani abu ta yi ajalin rayukan bayin Allah

Ya sanar da cewa gwamnatin jihar Kaduna ta samu tallafin dala miliyan 28 daga kasar Kuwait domin magance matsalar yara masu gararanba a tituna ba sa zuwa makaranta.

Sanata Sani ya jaddada bukatar a samar da shugabanci na gari, inda ya ce yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar abin damuwa ne da ke bukatar kulawa cikin gaggawa.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

Kotun ta yanke hukunci a shari'ar tsohon hafsan NAF

A wani rahoton kuma Babbar kotun tarayya ta yanke hukunci kan ƙarar da ake tuhumar tsohon hafsan sojin NAF, Adesola Amosun, da wawure N21.5bn.

Hukumar yaƙi da rashawa EFCC ce ta gurfanar Amosun tare da wasu mutum biyu bisa tuhumar halasta kuɗin haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262