‘Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Fada Sun Harbe Sarki, An Yi Awon Gaba da Mai Dakinsa

‘Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Fada Sun Harbe Sarki, An Yi Awon Gaba da Mai Dakinsa

  • Olukoro na kasar Koro ya riga mu gidan gaskiya a sakamakon wani hari da aka kai har fadarsa
  • ‘Yan bindiga sun kashe Mai martaba Janar Segun Aremu, ana tunanin an yi garkuwa da matarsa
  • Jami’an tsaro sun tabbatar da lamarin, an yi alkawarin cafko wadanda suka kashe Sarkin a Kwara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kwara - ‘Yan bindiga sun kai hari a daren yau a fadar Mai martaba Sarkin Koro a karamar hukumar Ekiti da ke jihar Kwara.

Rahoton Daily Trust ya ce ‘yan bindigan sun harbe Mai martaba Janar Segun Aremu mai ritaya wanda shi ne Olukoron Koro.

An kashe Sarki
‘Yan bindiga sun kashe Sarki a Kwara Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An kashe Sarki, an dauke matarsa a garin Ekiti

Miyagun ba su tsaya nan ba, sun dauke matar marigayi Janar Segun Aremu, sannan sun yi awon gaba da wasu mutane biyu.

Kara karanta wannan

An cusa Tinubu a lungu, ‘yan bindiga sun nemi N100m kafin sakin ‘yan makarantan Ekiti

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Kwara, Toun Ejire-Adeyemi ta sanar da aukuwar lamarin da safiyar ranar Juma’a.

Ejire-Adeyemi ta ce an aika dakaru domin ganin an cafko wadanda suka yi ta’adin.

Jawabin 'yan sandan jihar Kwara

"Muna tabbatarwa al’umma cewa za ayi bakin kokari wajen tabbatar da an yi gaggawar hukunta wadanda suka yi laifin.
An tsaurara matakai a yankin Koro, ana tattara jami’ai domin su ingnata tsaro domin tabatar da kariya ga mazaunan.

- Toun Ejire-Adeyemi

Gwamna ya aiko ta'aziyyar rasa Sarki

Leadership ta rahoto ‘yar sandar tana kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu, a ba jami’an tsaro hadin-kai wajen yin bincike.

Mai girma gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya yi Allah-wadai da wannan mummunan hari, ya ce dole a dauki matakai.

Gwamnan jihar Kwara ya fitar da ta’aziyya ne ta bakin sakataren labaransa, Rafiu Ajakaye.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da fusatattun matasa suka kona gidan babban basarake, an yi karin bayani

Matsalar tsaro ta shigo Kwara

Jaridar ta ce Koro tana makwabtaka da yankunan Irele/Oke Ako/Ipao/Oke Aiyedun da Ikole inda ake da matsalar tsaro.

Kwanan nan aka ji labarin an kashe wasu sarakuna biyu a jihar Ekiti a yankin.

Ana cikin rashin tsaro a Najeriya

Kuna da labari ana neman mutanen da aka sace daga makaranta bayan ‘yan bindiga sun kashe wasu Sarakuna a Najeriya.

Duk abin da yake faruwa, Shugaba Bola Tinubu yana waje, sai a cikin watan nanzai dawo, wasu sun soki zamansa a Faransa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel