Asirin Waɗanda Suka Kashe Sarakuna Biyu a Najeriya Ya Fara Tonuwa, An Kama Mutum 13

Asirin Waɗanda Suka Kashe Sarakuna Biyu a Najeriya Ya Fara Tonuwa, An Kama Mutum 13

  • Jami'an ƴan sanda sun cafke mutane 13 da ake zargi da hannu a kisan sarakuna biyu a jihar Ekiti
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta kasa, Muyiwa Adejobi, ya ce waɗanda aka kama suna ba da haɗin kai a aikin bincike
  • Ya bayyana cewa sufetan ƴan sanda na kasa ya tura AIG zuwa jihar domin ceto ɗalibai da malaman da aka sace

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce dakarunta sun kama wasu mutane 13 da ake zargi da hannu kisan sarakunan gargajiya biyu a jihar Ekiti.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanda ta kasa, Muyiwa Adejobi, shi ne ya bayyana haka a cikin shirin Channels tv mai taken, 'Siyasa a Yau' ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Dakarun ƴan sanda sun yi ƙazamin gamurzu da gungun ƴan bindiga, sun samu gagarumar nasara

Sufetan ƴan sanda da gwamnan Ekiti.
Mun kama mutum 13 da ake zargi da hannu a kisan sarakuna a Ekiti, Yan sanda Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

A rahoton Sahara Reporters, ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ya zuwa yanzu dai an kama mutane 13 da ake zargi da hannu a wannan lamarin. Kuma muna da tabbacin za mu cafke karin wadanda ake zargi."
"Muna aiki tare da su (wadanda ake tuhuma) kuma suna ba mu bayanai masu inganci da kuma masu amfani. Muna da tabbaci da yaƙinin kama duk masu hannu kuma mu gurfanar da su."

An tura AIG zuwa jihar Ekiti

Adejobi ya kuma ƙara da cewa Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya tura mataimakin sufeto Janar na ‘yan sanda (AIG) zuwa jihar ta Kudu maso Yamma.

A cewarsa, an tura AIG zuwa jihar Ekiti ne domin zaƙulo makasa da sauran masu aikata ayyukan ta'addancin da zasu naƙasa jihar.

Sarakunan biyu, Onimojo na Imojo-Ekiti, Oba Olatunde Olusola; da Elesun na Esun-Ekiti, Oba David Ogunsola, an kashe su ne a lokacin da suke dawowa daga wani taro a Irele-Ekiti ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Gwamnan arewa ya cire tsoro, ya faɗi abu 1 da ƴan Najeriya zasu yi su samu sauƙi da ci gaba

Zamu kwato ɗaliban za aka sace - Ƴan sanda

Kakakin ƴan sanda, Adejobi ya kuma ce rundunar ‘yan sandan ta tura jirgi mai saukar ungulu da motoci masu sulke zuwa jihar domin kakkaɓe yan ta'adda.

Haka zalika ya tabbatar wa mazauna jihar cewa za a kubutar da dalibai da malaman da aka yi garkuwa da su a kusa da yankin Eporo-Ekiti na jihar.

Sojoji sun ceto mutum 3

A.wani rahoton kuma Sojojin Najeriya sun yi artabu yan bindiga, sun kwato mutum uku da suka sace a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

A wata sanarwa da rundunar Birged ta 6 ta fitar, ta ce sojojin sun tari ƴan ta'addan ne bayan tattara sahihan bayanan sirri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel