Karshen Ƴan Bindiga Ya Zo: Gwamnan Arewa Ya Ƙaddamar da Rundunar da Za Ta Kakkaɓe Ƴan Bindiga

Karshen Ƴan Bindiga Ya Zo: Gwamnan Arewa Ya Ƙaddamar da Rundunar da Za Ta Kakkaɓe Ƴan Bindiga

  • Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya ɗauki ɗamarar yaƙar ƴan bindigan da suka addabi jihar
  • Gwamnan ya ƙaddamar da sabuwar rundunar 'Community Protection Guards' wacce za ta yi fito na fito da ƴan bindiga a jihar
  • Rundunar wacce aka fi sani da Askarawan Zamfara ta ƙunshi jami'ai 2,645 waɗanda aka zaɓo su daga ƙananan hukumomi 14 na jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta ƙaddamar da rundunar 'Community Protection Guards' (CPG) mai ɗauke da jami'ai 2,645 da nufin yaƙi da ƴan bindiga da sauran laifuka da suka addabi jihar.

Jami’an tsaron waɗanda da aka fi sani da Askarawan Zamfara an yi nufin su taimaka wa sauran jami’an tsaro wajen daƙile ƴan bindiga da sauran laifuka a jihar, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Sojoji sun fagargaji 'yan ta'adda a Katsina, sun halaka da dama

Gwamna Dauda ya kaddamar da rundunar tsaro
Gwamna Dauda ya kaddamar da sabuwar rundunar Askarawan Zamfara Hoto: @daudalawal
Asali: Twitter

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Dauda Lawal ya ce gwamnatin jihar ta sanya maƙudan kuɗaɗe a fannin tsaro a ƙoƙarinta na ganin an kawo ƙarshen matsalar ƴan bindiga a jihar, rahoton Vanguard ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Don haka gwamnan ya buƙaci jami’an CPG da su mayar da biki ta hanyar dagewa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Zamfara.

Gwamnonin Arewa sun duƙufa wajen daƙile matsalar tsaro

Gwamnan jihar Katsina Dr Umar Dikko Radda ya ce gwamnonin Arewa sun duƙufa wajen magance matsalolin tsaro da tattalin arziki da suka addabi yankin.

Shi ma da yake nasa jawabin, tsohon mai baiwa tsohon shugaban ƙasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida shawara kan harkokin tsaro, Janar Aliyu Muhmmad Gusau ya ce yaƙi da rashin tsaro dole ne ya kasance tare da ingantattun tsare-tsare da za su inganta rayuwar al’umma.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara kan ƴan ta'adda, sun sheƙe masu yawa

Janar Gusau ya bayyana cewa galibin laifukan da ake aikatawa suna da alaƙa kai tsaye da fatara da rashin aikin yi musamman a tsakanin matasa.

Gwamnatin jihar Zamfara ta samar da wasu motocin sintiri da babura ga jami’an CGP domin gudanar da ayyukansu cikin sauƙi.

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani mazaunin birnin Gusau, Jamilu Abdullahi, wanda ya yaba da wannan namijin ƙoƙarin da gwamnan ya yi.

Ya bayyana cewa samar da wannan rundunar zai taimaka sosai wajen yaƙar ƴan ɓindiga a jihar, domin sun samu horo da kayan aikin da suka dace.

Ya shawarci gwamnan da ya ƙara yawansu zuwa nan gaba domin ganin an kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar.

Gwamnan Katsina Ya Ƙaddamar da Rundunar Tsaro

A baya rahoto ya zo cewa gwamnan jihar Katsina, Dr. Dikko Umaru Radda ya ƙaddamar da sabuwar rundunar tsaron al'umma a jihar.

Gwamnan ya ƙaddamar da rundunar ne domin yin yaƙi da matsalar rashin tsaro wacce ta addabi jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel