Rahoto: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane 17, 000 a Karkashin Buhari da Tinubu

Rahoto: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Mutane 17, 000 a Karkashin Buhari da Tinubu

  • An yi wani taron manema labarai inda aka gabatar da rahoton halin rashin tsaro da ake fama da shi
  • Kungiyoyi masu zaman kansu sun ce mutane kusan 20, 000 sun fada hannun masu yin garkuwa
  • Daga Mayun bara zuwa farkon shekarar nan, ana da labarin rayuka kusan 2, 500 da aka rasa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Kungiyoyi masu zaman kansu a karkashin inuwar Civil Society Joint Action Group sun yi magana game da batun rashin tsaro.

A wani taron manema labarai da suka kira a garin Abuja, kungiyoyin sun ce an dauke mutane akalla 17, 469 a cikin shekaru biyar.

Bola Tinubu da Muhammadu Buhari
Bola Tinubu da Muhammadu Buhari sun gaza magance matsalar 'yan bindiga Hoto: @BashirAhmaad, @Dolusegun16
Asali: Twitter

Kungiyoyin sun ce wannan shi ne adadin Bayin Allah da aka yi garkuwa da su domin karbar kudin fansa daga 2019 zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Kudin Fansa: Masu garkuwa suna barazanar hallaka mutanen Abuja 11 da aka sace

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga a zamanin Tinubu

A taron ‘yan jaridar, kungiyoyin sun ce ‘yan bindiga sun hallaka mutane 2, 423 daga lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya hau kan mulki.

Bayan haka, ana da lissafin mutane 1, 872 da aka yi awon gaba da su a watanni takwas.

Shugaban CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani ya yi jawabi a madadin sauran kungiyoyin, ya bada rahoton ta’adin da aka yi a kasar.

'Yan bindiga sun gagari gwamnatoci?

Auwal Musa Rafsanjani ya yi ikirarin an hallaka rayuka 24, 816 a karkashin gwamnatoci ukun Muhammadu Buhari da Bola Tinubu.

A tsakanin wannan lokaci, an dauke mutane 15,597 domin a karbi kudin fansa. 90% na abubuwan da suka faru duk a gwamnatin baya ne.

Rashin tsaro yana shiga birane

90% na ta'adin da suka auku ne aka samu bayan Bola Tinubu ya shiga ofis a Mayun 2023. Zuwa yanzu barnar tana kara shiga cikin birane.

Kara karanta wannan

An kama 1 daga kasurguman 'yan bindigan da suka sace Nabeeha da 'yan uwanta a Abuja

‘Yan bindiga sun addabi Abuja da bangarorin Kudancin Najeriya da abin bai yi kamari ba. Hakan ya jawo an hurowa gwamanati wuta.

'Yan bindiga: Meya dace da gwamnati

Shugaban Transparency International a Najeriya, Auwal Rafsanjani ya kawo shawara gwamnati ta sa dokar ta-baci a bangaren tsaro.

Rafsanjani yana ganin lamarin rashin tsaro ya kai matakin da dole a tashi tsaye a yanzu.

A makon nan aka samu labari ‘yan bindiga sun hallaka wasu sarakunan gargajiya a Ekiti, gwamnati ta sha alwashin tona asirin miyagun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel