Gwamnan PDP Ya Fusata, Ya Sanya Dokar Kulle a Garuruwa Biyu Faɗa Ya Kaure

Gwamnan PDP Ya Fusata, Ya Sanya Dokar Kulle a Garuruwa Biyu Faɗa Ya Kaure

  • Gwamna Ademola Adeleke ya sanya dokar kulle a garuruwa biyu na jihar Osun kan rikicin da ya ɓarke a tsakaninsu
  • A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai ya fitar, ya ce dokar zata fara aiki ne nan take daga karfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma
  • Gwamnatin Osun ta ce zata kafa tawagar haɗin guiwa a tsakanin yankunan biyu domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Gwamnatin jihar Osun ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ademola Adeleke ta ƙaƙaba dokar zaman gida daga 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma a Ifon da Ilobu.

Channels tv ta tattaro cewa wannan na kunshe ne a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma na jihar, Oluomo Kolapo Alimi, ya rattaba hannu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya bayyana abu 1 da ya hana kawo karshen matsalar tsaro a jiharsa

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke.
Gwamna Adeleke Ya Sanya Dokar Kulle a Garuruwa Biyu a Jihar Osun Hoto: Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Ya ce gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya ya dawo a ƙauyukan biyu masu faɗa da juna, wanda rikici ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a tsakani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwan dokar hana fitan, "za ta fara aiki ne nan take daga yau Talata 30 ga watan Janairu, 2024 a kauyukan biyu masu rashin jituwa da juna."

Wane matakai gwamnati ta ɗauka kan rikicin kauyukan?

Domin dakile duk wani tashin hankali da ka iya faruwa nan gaba, gwamnatin Osun ta ce za ta kafa rundunar hadin gwiwa da zata ƙunshi masu ruwa da tsakin garuruwan biyu.

A cewarta, tawagar haɗin guiwar da za a kafa zata kunshi sarakunan gargajiya na Ifon, Ilobu da kuma Erin Osun, rahoton Vanguard.

Bayanai sun nuna cewa an kara girke ƙarin jami'an tsaro da suka haɗa da dakarun sojoji, yan sanda da jami'an sibil defens a yankunan biyu domin dawo da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya kori wasu hadimai daga aiki a gwamnatinsa, ya naɗa sabbi nan take

A ƙarshe, Gwamnatin Adeleke ta gargaɗi mazauna waɗannan yankuna cewa duk wanda ya shiga hannu kan laifin tada zaune tsaye zai ɗanɗanar kuɗarsa ko waye shi.

An kashe shugabannin matasa 2 a Delta

A wani rahoton na daban Wasu mutane ɗauke da bindigu sun halaka shugabannin matasa biyu kisan gilla a jihar Delta ranar Litinin.

Tsohon sanata a jihar, Chief Ighoyota Amori, ya yi tir da wannan kisan, inda ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da sauran al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262