Yaki da ta'addanci a Najeriya
Gwamnatin jihar Sokoto ta amince da gina titin hanya wanda zai ba jami'an tsaro damar zuwa maboyar 'yan bindiga. Gwamnan ya ce ya shirya kare rayuka da dukiyoyi.
Wasu miyagu sun kai harin rashin tausayi kan wani dan kungiyar mafarauta a Katsina, inda su ka kashe shi tare da kone gawarsa tare da sace iyalansa.
Hukumar ƴan sandan Najeriya ta gayyaci shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa, Joe Ajaero kan zarge-zarge da suka haɗa da ɗaukar nauyin ta'addanci da sauransu.
Miyagu sun hana mazauna kananan hukumomi biyu; Musawa da Kankia a jihar Katsina sakat, yayin da su ka kai hari tare da sace mata da yara da magidanta.
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bijiro da wata manhaja mai suna mobilizer da za ta ba wa yan kasa damar mika sakon ta'addanci ko rashin tsaro a yankunansu.
Basarake a Takum da ke jihar Taraba, Barista Sopiya Ahmadu Gboshi ya nuna damuwa kan rasa rayuwa a yankin inda ya zargi yan jihar Benue da kara rashin tsaro.
Matafiya sun yi kicibis mugun gamo da 'yan ta'adda hanyar Gusau-Funtua, inda miyagun su ka ɗauke fasinjojin mota uku,tare da sace wasu a Unguwar Chida.
Rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya ta bayyana cewa ƴan ta'adda biyar sun baƙunci lahira yayin da dakaru suka kai samame sansanin ISWAP a Bama da ke jihar Borno.
Yan bindiga sun yi ajalin mutane shida, sannan sun yi awon gaba da wasu mutane 26 a hare-haren da suka kai kauyuka huɗu a karamar hukumar Kauru ta Kaduna.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari